Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-01@17:42:16 GMT

‘Yan Sanda Sun Kamu A Kano

Published: 28th, January 2025 GMT

‘Yan Sanda Sun Kamu A Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta samu gagarumar nasara wajen yaki da miyagun laifuka, inda ta kama wasu da ake zargi da aikata manyan laifuka da dama.

 

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Salman Dogo Garba ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan Bompai Kano.

 

Ya ce rundunar ta kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu wajen yin garkuwa da kuma kashe Alhaji Atiku Mu’azu, mai shekaru 64 da haihuwa mazaunin Janbulo, Kano.

 

Wadanda ake zargin, Abubakar Hassan (wanda aka fi sani da Captain), Adamu Abubakar Adam, da Alhaji Hamisu (wanda aka fi sani da Bakin Bross), an kama su ne bayan wani ci gaba da bincike da jami’an leken asiri suka yi.

 

A wani labarin kuma wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan Alhaji Auwalu da ke Sabuwar Unguwa Garo a karamar hukumar Kabo a Kano, inda suka yi masa fashin Naira miliyan 8 tare da yin garkuwa da ‘yarsa Zainab Aliyu mai shekaru 16.

 

CP Salman Dogo Garba ya ci gaba da cewa, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike domin ceto wanda aka kashe tare da damke wadanda suka aikata laifin.

 

Kwamishinan ‘yan sandan ya ci gaba da bayyana cewa, a wani samame na daban, rundunar ‘yan sandan ta kama wasu mutane 17 da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da suka abkawa Hotoro a Kawo Kano, inda suka farfasa shaguna da motoci, tare da far wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

 

“An kuma kama wasu mutane uku da ake zargin ‘yan fashi da makami ne da laifin kai hari ga wasu mutane biyu da ba su ji ba ba su gani ba, tare da yi musu fashin wayoyin hannu guda 200 a unguwar Yankatsari da ke Kano.

 

CP Salman Dogo Garba ya bukaci jama’a da su kiyaye da taka tsantsan, kuma su kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su ko kuma ta lambobin hukumar: 08032419754, 08123821575, 09029292926.

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Yansanda wasu mutane

এছাড়াও পড়ুন:

A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi

A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan Tehran dubban daruruwan mutanen suka fito zuwa babbar masallacin Imam Khumaini dake tsakiyar birnin Tehran inda suka gudanar da sallah mai raka’o’I biyu tare da jagorancin Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Imam Sayyid Aliyul Khamina’e.

Duk da cewa ana samun babbanci tsakanin musulmi kan ranar ajiye azumun amma akalla ba wanda zai yi azami kasa da kwanaki 29.

A cikin watan dai, musulmi sukan yawaita karatun alkur\ani mai girma da kuma kokarin sanin ma’anarsa da kuma zrfafa tunani a cikinsa.

Har’ila yau watan ne na yawaita sadaka na abinci da kuma duk abinda zai taimakawa masu karamin karfi a tattalin arziki.

Musulmi sukan yawaita addu’a da neman gafarar All..a kan zunubban da suka aiakata sannan suna yawaita salloli.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda
  • Nigeria: Zazzabin “Lassa” Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 118 Tun Farkon Wannan Shekara
  • ‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa
  • Gwamna Edo Okpebholor Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  • Yadda ‘Yan Banga A Edo Suka Yi Sanadin Kashe Matafiya Mafarauta 16 – Direban Motar
  • A Yau Litinin Ce Aka Gudanar Da Sallar Edi Da Bukukuwan Sallah A Nan Iran Da Wasu Kasashen Musulmi
  • Matashi ya kashe jami’in tsaron Sarki Sanusi II a Kano
  • Cutar Mashaƙo Ta Ɓarke A Legas, Mutane 10 Sun Kamu
  • Kashe Matafiya: Gwamnatin Kano Ta Aika Tawaga Zuwa Edo