Shin sojoji sun kama Bello Turji ba?
Published: 28th, January 2025 GMT
Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji.
Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu ƙamshin gaskiya a labarin kama Turji, amma suna neman shi ruwa a jallo.
A jawabinsa ga ’yan jarida, Edward Buba ya shawarci ’yan Najeriya su yi watsi da labarin ƙaryan, da cewa, “duk labarin da ake bazawa game da kama Bello Turji ƙanzon kurege ne.”
Tun bayan da sojoji suka tsananta ragargazar sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, musamman Jihar Zamfara inda ya fi yin ɓarna, aka daina jin ɗuriyarsa.
A makon jiya sojoji suka kashe ɗan Bello Turji, da manyan yaran ɗan ta’addan, ciki har da babban mataimakinsa da manyan kwamadoninsa bakwai.
Bello Turji na daga cikin manyan ’yan ta’addan da a tsawon shekaru suka addabi jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da Kaduna da Kebbi da hare-hare inda suke yi wa jama’a kisan gilla tare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da sace dabbobi da ƙona dukiyoyi.
A yayin da jami’an tsaro ke faɗi-tashin murƙushe su, lamarin ya sake ɗaukar sabon salo bayan ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ’yan ta’addan ƙasashen waje, wadda aka fi sani da Lakurawa, musamman a jihohin Sakkwato da Kebbi.
Aƙalla shekara goma ke nan da ’yan bindiga suka addabi yankin Arewa maso Yamma, inda suka rabba dubban ɗaruruwan mutane da garuruwansu, suka hana harkokin noma da kasuwanci, baya ga karɓar daruruwan miliyoyi a matsayin kuɗin fansa ko haraji da suka ƙaƙaba ba al’umma.
Ko a kwanakin baya, wasu labarai sun yi yawo a kafofin sada zumunta cewa dakarun sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar sun kama Bello Turji bayan da sojojin Najeriya suka fatattaki shi. Amma daga baya ta bayyana cewa labarin shaci-faɗi ne.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Edward Buba Sakkwato Tsaro Turai Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Al-Houthi : Isra’ila Na fakewa Da Goyan Bayan Amurka Tana Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza.
Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. »
Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. »
Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga yankin Rafah. »
Al-Houthi ya kara da cewa: Haka nan makiya yahudawan sahyoniya ba su janye gaba daya daga kudancin kasar Labanon ba, wanda ya zama mamaya da kuma barazana ga al’ummar kasar Lebanon da kuma keta hurimin kasar. »
Zamu zura ido mu gani, kuma dole ne mu kasance cikin shiri,” in ji jagoran kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen.