Aminiya:
2025-04-23@02:46:37 GMT

Gaskiyar batun kama Bello Turji ba —Sojoji

Published: 28th, January 2025 GMT

Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta yi tsokaci a karon farko kan  labarin da ke yawo cewa sojojinta sun kama ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji.

Rundunar tsaron ta sanar da gaskiyar lamarin ne bayan raɗe-raɗin kama Bello Turji ya karaɗe kafofin sada zumunta.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba, ya sanar cewa babu ƙamshin gaskiya a labarin kama Turji, amma suna neman shi ruwa a jallo.

A jawabinsa ga ’yan jarida, Edward Buba ya shawarci ’yan Najeriya su yi watsi da labarin ƙaryan, da cewa, “duk labarin da ake bazawa game da kama Bello Turji ƙanzon kurege ne.”

Tun bayan da sojoji suka tsananta ragargazar sansanonin ’yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas, musamman Jihar Zamfara inda ya fi yin ɓarna, aka daina jin ɗuriyarsa.

A makon jiya sojoji suka kashe ɗan Bello Turji, da manyan yaran ɗan ta’addan, ciki har da babban mataimakinsa da manyan kwamadoninsa bakwai.

Bello Turji na daga cikin manyan ’yan ta’addan da a tsawon shekaru suka addabi jihohin Zamfara da Katsina da Sakkwato da Kaduna da Kebbi da hare-hare inda suke yi wa jama’a kisan gilla tare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da sace dabbobi da ƙona dukiyoyi.

A yayin da jami’an tsaro ke faɗi-tashin murƙushe su, lamarin ya sake ɗaukar sabon salo bayan ɓullar wata sabuwar ƙungiyar ’yan ta’addan ƙasashen waje, wadda aka fi sani da Lakurawa, musamman a jihohin Sakkwato da Kebbi.

Aƙalla shekara goma ke nan da ’yan bindiga suka addabi yankin Arewa maso Yamma, inda suka rabba dubban ɗaruruwan mutane da garuruwansu, suka hana harkokin noma da kasuwanci, baya ga karɓar daruruwan miliyoyi a matsayin kuɗin fansa ko haraji da suka ƙaƙaba ba al’umma.

Ko a kwanakin baya, wasu labarai sun yi yawo a kafofin sada zumunta cewa dakarun sojin ƙasar Jamhuriyar Nijar sun kama Bello Turji bayan da sojojin Najeriya suka fatattaki shi. Amma daga baya ta bayyana cewa labarin shaci-faɗi ne.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Edward Buba Sakkwato Tsaro Turai Zamfara

এছাড়াও পড়ুন:

Leicester City Ta Koma Gasar Yan Dagaji Bayan Shan Kashi A Hannun Liverpool

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta koma gasar yan dagaji ta Championship bayan da tayi rashin nasara a guda a wasanta da Liverpool.

Leicester wadda ta lashe gasar Firimiya a shekarar 2016 ta samu maki 18 kacal a wasanni 33 da ta buga, ta zura kwallaye 27 yayinda aka zura mata kwallaye 73 a ragarta, Leicester ta koma gasar Championship duk da cewar akwai sauran wasanni 5 da su ka rage ba a buga ba a gasar Firimiya ta bana.

Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila? Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya

Kocin Leicester Ruud Van Nistelrooy ya karbi ragamar horarwar Leicester a watan Janairu bayan raba gari da kungiyar ta yi da Steve Cooper, amma kuma abinda ake gujewa ya faru ga kungiyar wadda ke matsayi na 19 akan teburin gasar Firimiya.

Trent Alexander Arnold ne ya ci wa Liverpool kwallonta, wadda kuma ta kasance kwallo daya tilo a aka ci a wasan, zuwan Leicester gasar yan dagaji ya sa ta kasance kungiya ta biyu da ta koma bayan Southampton a bana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ECOWAS Zata YI Taro A Ghana Don Tattauna Batun Niger, Mali Da Burkina Faso
  • Sojoji Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Garkuwa Da Mutane Tare Da Kwato Makamai A Kano
  • Iran Ta Jaddada Matsayinta Kan Batun Tace Sinadarin Yuranium A Batun Tattaunawa Da Amurka
  • Sojoji Sun Daƙile Harin Boko Haram A Yobe
  • Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
  • Zaɓen 2027: An soma liƙa fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamnan Bauchi
  • Miji ya yi wa matarsa saki 3 a ofishin ’yan sanda
  • Leicester City Ta Koma Gasar Yan Dagaji Bayan Shan Kashi A Hannun Liverpool
  • An Gayyaci Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Aragchi Taron Makamashin Nukliya A Amurka
  • Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu