‘Yan Tawayen Sudan Sun Kona Wani Bangaren Matatar Mai Ta Al-Jili Da Ke Birnin Khartoum Bahri
Published: 28th, January 2025 GMT
Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Kungiyar Rapid Support Forces sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum na kasar Sudan
Mayakan kungiyar dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan matatar mai ta Al-Jili da ke birnin Khartoum Bahri, wadda ita ce matatar mai mafi girma a kasar Sudan, wadda take samar da man fetur a yawancin jihohin kasar ta Sudan, duk kuwa da cewa kwararru sun tabbatar da takaitar barnar da aka yi wa matatar Man duk da tashin bam da aka samu a cikin matata da ya tilasta dakatar da duk wani aiki a cikinsa.
Sojojin Sudan sun yi amfani da dama a lokacin da dakarun kungiyar Rapid Support Forces suke fita daga matatar man, zuwa shiyar lardin Darfur domin neman mafaka mafi aminci, inda sojojin suka yi musu luguden bama-bamai ta hanyar jiragen saman yaki, wasu rahotonni suna cewa; Har yanzu Dakarun kai daukin gaggawan ne suke iko da mafi yawan jihohin lardin Darfur da ke arewacin kasar ta Sudan.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Yeman : Sojojin Amurka sun kai wani gagarumin farmaki kan lardunan Sanaa da Hudaidah
Mutane da dama ne suka mutu sannan wasu sun jikkata sakamakon wasu sabbin hare-hare da jiragen yakin Amurka suka kai kan wasu yankuna na kasar Yemen.
A daren jiya wayewar yau Lahadi, sojojin Amurka sun kai hare-hare ta sama akalla 20 a Sanaa babban birnin kasar Yemen, da kuma yammacinta da gabashi da kuma kudancin kasar.
Hare-haren na zuwa ne a daidai lokacin da mahukuntan kasar Yemen suka sanar a ranar Asabar cewa kimanin mutane 80 ne suka mutu, yayin da wasu 150 suka samu raunuka sakamakon harin da Amurka ta kai a ranar Juma’a a tashar mai na Ras Issa da ke birnin Hudaidah.
Hare-haren na Amurka a Yemen sun kara gurgunta halin da kasar ta Yemen ke ciki.
Babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana matukar damuwarsa game da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, ciki har da hare-haren da aka kai a kusa da tashar ruwan Ras Issa.
Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Stéphane Dujarric, ya bayyana a wata sanarwa jiya Asabar cewa, “Guterres ya damu matuka da hare-haren da Amurka ta kai a ranakun 17 da 18 ga watan Afrilu a ciki da wajen tashar jiragen ruwa na Ras Issa na kasar Yemen, wanda ya yi sanadin jikkatar fararen hula da dama, ciki har da ma’aikatan agaji biyar.