Sanatan Amurka Ya Yi Kakkausar Suka Kan Batun Tilastawa Falasdinawa Yin Gudun Hijira Daga Gaza
Published: 28th, January 2025 GMT
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa
Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci.
A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza zuwa kasashen da suke makwabta da su kamar Masar da Jordan, yana mai cewa Zirin Gaza ba wuri ne da ya dace da zamansu ba, sakamakon kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi musu.
Sanders ya ce: “Dole ne duk wani Ba’amurke ya yi Allah wadai da wannan mugun ra’ayi na Trump na korar Falasdinawa daga tushensu,” yana mai jaddada cewa: Kiran da Trump ya yi na tilastawa miliyoyin Falasdinawa kaura daga Gaza zuwa kasashe makwabta yana da sunan da ya dace da shi: wato “shafe wata kabilanci daga tushe karkashin laifin yaki.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Falasdinawa da
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Ta Ce Tattaunawa Da Amurka Tare Da Mai Shiga Tsakani Na Gaba, Ya Danganci Matakan Da Ta Dauka Kan Iran
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka amsar wasikar da ta aiko mana, inda a cikinta, muka kara jaddada cewa babu wata tattaunawa kai tsaye da Amurka, kuma an tura wasikar ta inda na Amurkan ta fito wato ta kasar Omman. Don haka muna jiran matakan da Amurka zata dauka a kan amsar.
Daga karshe shugaban ya kammala da cewa duk wata mu’amala da gwamnatin kasar Amurka ba zai taba yiyuwa kai tsaye ba, wannan kuma saboda mummunan tarihin da Amurkawa suke da shin a karya al-kawali a duk wata yarjeniyar da aka cimma da ita a baya.
Ya dukkan tarihin JMI bata taba sabawa alkawalin da ta dauka da wata kasa ba, amma gwamnatin Amurka kuma tana da mummunan tarihi na sabawa alkawali don haka a halin yanzu ya rage mata ta sauya halayenta.