Dan Majalisar Dattijan Amurka Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Trump Na Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Published: 28th, January 2025 GMT
Dan Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana kiran da shugaban Amurka ya yi tilastawa Falasdinawa gudun hijira Falasdinawa da cewa kokari ne na shafe wata al’umma daga kan doron kasa
Dan Majalisar Dattawan kasar Amurka Sanata Bernie Sanders a jiya Litinin ya fara mayar da martani ga shugaban Amurka Donald Trump inda ya bayyana kiran da Trump ya yi na korar Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa kasashen da ke makwabtaka da su a matsayin kokarin “Shafe wata al’umma ce daga kan doron kasa kuma laifin yaki ne” inda ya bukaci dukkan Amurkawa da su yi Allah wadai da wannan furuci.
A ranar Asabar da ta gabata ce shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar mayar da Falasdinawa daga zirin Gaza zuwa kasashen da suke makwabta da su kamar Masar da Jordan, yana mai cewa Zirin Gaza ba wuri ne da ya dace da zamansu ba, sakamakon kisan kiyashin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi musu.
Sanders ya ce: “Dole ne duk wani Ba’amurke ya yi Allah wadai da wannan mugun ra’ayi na Trump na korar Falasdinawa daga tushensu,” yana mai jaddada cewa: Kiran da Trump ya yi na tilastawa miliyoyin Falasdinawa kaura daga Gaza zuwa kasashe makwabta yana da sunan da ya dace da shi: wato “shafe wata kabilanci daga tushe karkashin laifin yaki.”
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Falasdinawa da
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta kakaba wa Iran sabbin takunkumai duk da tattaunawa
Gwamnatin Amurka ta kakabawa kamfanonin kasar Iran sabbin takunkumi, duk da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar.
Ofishin kula da kadarorin waje na ma’aikatar baitul malin Amurka (OFAC) ya sanar a cikin wata sanarwa jiya Talata cewa, ya kara sunan wani dan kasuwa dan kasar Iran, Seyyed Assadollah Emamjomeh da kamfaninsa cikin jerin takunkumin da aka kakabawa Iran bisa zarginsu da hannu wajen fitar da danyen mai da iskar gas a Iran.
Amurka ta yi zargin cewa Emamjomeh da mukarrabansa ne ke da alhakin jigilar danyen mai na iran da aka kiyasta ya kai daruruwan miliyoyin daloli zuwa kasuwannin kasashen waje.
Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta yi zargin cewa kamfanin Emamjomeh ya fitar da dubunnan kayayyaki daga Iran zuwa Pakistan tare da gudanar da hada-hadar kudi na miliyoyin daloli.
Sabon takunkumin dai shi ne irinsa na bakwai da gwamnatin Amurka ta dauka kan Iran tun a ranar 4 ga watan Fabrairu, lokacin da shugaban Amurka Donald Trump ya zartar da dokar yin matsin lamba kan Tehran.
Sabbin takunkuman dai na zuwa ne a daidai lokacin da Iran da Amurka suka gudanar da shawarwari guda biyu domin warware sabanin da ke tsakaninsu dangane da shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya.