Aminiya:
2025-03-02@22:10:42 GMT

Jadawalin Gasar AFCON 2025 da za a fafata a Morocco

Published: 28th, January 2025 GMT

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka CAF, ta fitar da jadawalin ƙasashen da za su fafata a Gasar Kofin Nahiyyar Afirka AFCON wadda Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamba na bana.

An gudanar da bikin fitar da jadawalin ranar Litinin a Cibiyar Taro ta Ƙasa ta Mohammed V National da ke birnin Rabat a Morocco.

A soma duba watan Sha’aban ranar Laraba — Sarkin Musulmi Nijeriya na da arzikin da za ta riƙa ɗaukar nauyin tafiye-tafiyen Tinubu — Minista

Tawagogi biyu mafi ƙwazo a kowanne rukuni ne za su tsallaka kai tsaye zuwa mataki na gaba, sai kuma tawagogi huɗu mafi ƙwazo da suka zo a mataki na uku a duk cikin rukunan.

Morocco wadda wannan shi ne karo na farko da za ta kasance mai masaukin baƙi tun 1988, za ta jagoranci rukunin A, inda za ta ɓarje gumi da Mali da Zambia da kuma Comoros.

Masar da ta taɓa lashe gasar sau bakwai a tarihi, za ta kara ne da Afrika ta Kudu da Angola da kuma Zimbabwe a rukunin B.

Rukunin C kuwa wanda ya ƙunshi Nijeriya wadda ta lashe kofin sau uku, za ta yi karon-batta da Tunisia da Uganda da kuma Tanzania.

Senega da ta lashe gasar a shekarar 2021, za ta kara da Jamhuriyar Dimukaraɗiyar Congo da Benin da kuma Botswana wacce wannan ne karo na biyu da za ta halarci gasar.

Algeria ce ke jagorantar rukunin E wanda ya ƙunshi ƙasashen Burkina Faso da Equatorial Guinea da Sudan.

Cote d’Ivoire wacce ke kare kambin ta na rukuni F, tare da Kamaru da Gabon da kuma Mozambique.

A dai ranar 21 ga watan Disamba ne za a buɗe gasar da karawa tsakanin Morocco da Comoros, sai kuma a buga wasan ƙarshe a ranar 18 ga watan Janairun 2026.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Gobe Asabar 1 Ga Watan Ramadan 1446

Fadar mai alfarma sarkin Musulmi, ta sanar da ganin jinjirin watan Ramadan da maraicen Juma’ar nan a Sakkwato.

 

Cikin wata sanarwa da Mai Alfarma Sarkin Musulmin, Sa’ad Abubakar lll ya karanta a fadarsa, ya ce an ga watan a sassan ƙasar daban-daban.

 

Don haka ne ya ayyana ranar Asabar 1 ga watan Maris a matsayin 1 ga watan Ramadan 1446.

Nasiru Malami/Sakkwato

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ban fitar da ran lashe Premier League na bana ba — Arteta
  • Shin Liverpool Za Ta Kai Labari Ba Tare Da Muhammad Salah Ba?
  • Iran Ta Zama Zakara A Damben Gargajiya Ta 2025 UWW Wanda Aka Gudanar A Kasar Albaniya
  • Rasha Za Ta Bunkasa Kai Wa  Nahiyar Afirka Alkama
  • Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗin 2025 na N54.99trn
  • Tinubu ya sanya hannu a kasafin kuɗi na N54.99trn
  • Gobe Asabar 1 Ga Watan Ramadan 1446
  • An ga jinjirin watan Ramadan a Saudiyya 
  • Maraba Da Watan Ramadan
  • LEADERSHIP HAUSA Ta Bayyana Wadanda Suka Yi Nasara A Gasar Gajerun Labaran Soyayya