Hukumar Gidagen Radiyo Da Talabijin Na Kasar Iran Ta Bada Sanarwan Kama Dan Rahotonta A Kasar Falasdinu Da Aka Mamaye
Published: 28th, January 2025 GMT
A dai-dai lokacinda jijiyoyin wuya suke kara tashi tsakanin JMI ta kuma HKI, jami’an tsaron HKI sun kama daya daga cikin yan rahotomta sun tsare.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban hukumar gidajen radiyo da Talabijin ta kasar (IRIB), Peyman Jebelli yana fadar haka ya kuma kara da cewa dan rahoton hukumar baya Gaza, yana cikin kasashen Falasdinu da aka mamaye ne.
Labarin ya kara da cewa tun ranar da aka fara yakin tufanul Aksa a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 jami’an tsaron HKI sun kashe yan jaridu 205, sannan ta kama wasu 75, sannan har yanzun wasu 42 kuma tana tsare da su. Annan akalla 10 daga cikinsu tana tsare da su ne a karkashin dokannan da ake kira (administration datentiomn) wato tsarewa karkashin dokar masu iko.
Bisa bangare na 79 karkashin doka ta taron Geneva, yan jaridu wadanda suke aiki a cikin wurare masu hatsari su abin karewane kamar yadda ake bukatar a kare fararen hula, matukar basu dauki bangare a rikicin ba.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula Da Kasuwa: Adadin Kamfanoni Masu Zaman Kansu A Kasar Sin Ya Zarce Miliyan 57
Hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ya zarce miliyan 57 ya zuwa karshen watan Maris, wanda ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar baki daya. Kazalika, a rubu’i na farko, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu da aka kafa a kasar ya kai miliyan 1.979, wato karuwar kashi 7.1 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya zarce matsakaicin ci gaban da aka samu a shekaru ukun da suka gabata. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp