Sin Ta Yi Kira Ga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya Da Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Sudan
Published: 28th, January 2025 GMT
Mataimakin wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang ya ce, ya kamata kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta karfafa hadin gwiwa da kasar Sudan, inda kuma ya bukaci gamayyar kasa da kasa da ta kara taka rawar gani wajen sasanta rikici a kasar.
Geng Shuang ya bayyana haka ne jiya, yayin wani taro da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira don tantance rahoton da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta gabatar dangane da batun Darfur na kasar Sudan.
A cewar Geng, yayin da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke gudanar da bincike a kasar Sudan, ya kamata ta yi mu’ammala sosai da gwamnatin kasar Sudan, kafin daukar wani mataki, ta yadda za a tabbatar da daidaita matsalar kasar, da magance tsanantar rikicin da ake samu. Kana ya kamata a aiwatar da dokokin kasa da kasa cikin daidaito, ba tare da siyasantar da harkokin shari’a, da bambanta ma’auni bisa wurin da ake ciki ba. (Bello Wang)
কীওয়ার্ড: kasar Sudan
এছাড়াও পড়ুন:
Ba Za A Iya Dakile Ci Gaban Hakkin Dan Adam Na Xizang Da Kowace Irin Karya Ba
A bana aka cika shekaru 60 da kafuwar jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A ranar 28 ga watan Maris, wato ranar tunawa da ’yantar da miliyoyin bayi manoma a Xizang, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani mai taken “Ci gaban hakkin bil’adama a Xizang a sabon zamani”, wadda ta yi amfani da cikakkun bayanai na gaskiya don nuna yadda aka samu manyan sauye-sauye a jihar a cikin shekaru gommai da suka wuce. Takardar ta kuma shaida mana ma’anar “Jin dadin zama ga jama’a babban hakki ne na dan Adam”.
“Ci gaba da aka samu a Xizang ya wuce yadda na yi zato, kuma mutane a nan suna rayuwa irin ta zamani sosai.” Wannan shi ne yadda babban dan jaridar kafar watsa labarai ta 24NewsHD ta kasar Pakistan Ali Abbas ya fada bayan ziyararsa a jihar. A cewarsa, karin mutane a duniya sun fahimci cewa, don neman kawo baraka ga kasar Sin ne wasu kasashen yammacin duniya suke kara wa miya gishiri a batun hakkin bil’adama a Xizang. Sannan game da batun ko an kiyaye hakkin bil’adama da kyau ko a’a a Xizang, bayanan sun riga sun ba da kyakkyawar amsa a kai, kana hakikanan labarun zaman rayuwar jama’ar jihar su ma sun bayyana gaskiya, don haka babu wata karya da za ta iya rufe ko kuma goge ainihin halin da ake ciki a jihar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp