An Maka Gwamna Fintiri A Gaban Kotu Kan Ƙirƙiro Sabbin Masarautu A Jihar Adamawa
Published: 28th, January 2025 GMT
Da yake jawabi a taron manema labarai ranar Talata a Yola a madadin Masarautar Fufore, Alkasum Abba, ya ce kafa sabbin Masarautu abu ne wanda sam bai da ce ba kuma an aiwatar da tsarin ba bisa ka’ida ba.
Ya yi ikirarin cewa, sun yi iyakacin kokarinsu na neman tattaunawa da sulhu a kan lamarin da gwamnan jihar amma abin ya ci tura.
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Zamfara ta haramta taruka siyasa saboda tsaro
Gwamnatin Jihar Zamfara ta haramta gudanar da tarukan siyasa a faɗin jihar har sai abin da hali ya yi, domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wannan mataki ya biyo bayan wasu tashe-tashen hankula masu nasaba da siyasa, inda jam’iyyar adawa ta APC ta koka cewa an kai wasu daga cikin jami’anta hari.
Janar Musa ya fallasa ƙasashen da ke ɗaukar nauyin Boko Haram Kifi jinsin Shark ya fusata ya fasa rufin gida Dalilin Haramta Tarukan SiyasaBabban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Zamfara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Al’amuran Jama’a, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa an ɗauki mataki ne, sakamakon wata hatsaniya da ta auku a Ƙaramar Hukumar Maru.
Ya ce: “Daga yanzu, an haramta duk wani taro ko gangami da zai iya haddasa tashin hankali, musamman ganin yadda aka rasa rayuka da ƙone dukiya mai yawa a Ƙaramar Hukumar.”
Ya kuma ƙara da cewa wannan dakatarwa ba ta dindindin ba ce, illa dai mataki ne na wucin gadi domin kiyaye zaman lafiya a jihar.
Martanin Jam’iyyar APCA nata ɓangaren, jam’iyyar APC reshen Zamfara, ta soki matakin, inda ta bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne saboda tsoron ƙarfin jam’iyyar a jihar.
Mai magana da yawun jam’iyyar, Malam Yusuf Idris Gusau, ya ce: “Ai abin mamaki ne a ce an hana tarukan siyasa, domin ba gangamin yaƙin neman zaɓe aka shirya ba.
“Babu wata doka da ta hana tarukan jam’iyyu, don haka gwamnati ba ta da hurumin hana mu gudanar da harkokinmu na siyasa.”
Ya ƙara da cewa APC jam’iyya ce mai rijista a ƙasa, kuma mabiyanta suna bin doka ba tare da haddasa wata fitina ba.
Fargabar Ƙarin Tashin HankaliAna dai ganin wannan mataki na gwamnati da martanin APC na iya ƙara dagula lamarin siyasa a jihar.
Masana da masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin akwai buƙatar a samu tattaunawa tsakanin ɓangarorin biyu, tare da shiga tsakani da dattawa da jami’an tsaro domin hana rikicin ya tsananta.