CMG Ya Yi Nunin Fitilu A Jikin Manyan Gine-Ginen Afirka Ta Kudu Da UAE
Published: 29th, January 2025 GMT
Babban rukunin gidajen rediyo da telabijin na kasar Sin (CMG) ya yi wani nuni na musamman na fitilu a jikin wasu manyan gine-gine guda 2 na kasar Afirka ta Kudu da na kasar hadaddiyar daular Larabawa ta UAE.
Nunin fitilun da aka yi a jikin ginin “The Leonardo”, gini mafi tsayi a kasar Afirka ta Kudu dake birnin Johannesburg, ya kunshi alamun shagalin murnar bikin bazara na kasar Sin da CMG din ya tsara, da zane-zanen salon musamman na murnar bikin bazara na Sin, wadanda suka burge jama’ar birnin Johannesburg sosai.
A sa’i daya kuma, nunin fitilun na CMG shi ma ya hau bangon hasumiyar Burj Khalifa dake Dubai na kasar UAE, wadda ta kasance gini mafi tsayi a duniya. (Bello Wang)
এছাড়াও পড়ুন:
Bayan Hukuncin ‘Yansanda, Sarki Sanusi II Ya Soke Hawan Sallah
Sarkin Kano mai daraja ta daya wanda ya bayyana zaman lafiya a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, don haka, ya amince da janye duk wasu shirye-shiryen bikin hawan Sallah mai ban sha’awa, wanda ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da al’adu (UNESCO) ta bayyana a matsayin gadon bil’adama mara misaltuwa.
LEADERSHIP ta rawaito cewa, kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Adamu Bakori ne ya sanar da dakatar da bikin hawan Sallah, saboda barazanar tsaro da jami’an leken asiri suka rahoto a jihar.
Dangane da haka, Sarki Sanusi ya yi kira ga al’umma da su kasance masu zaman lafiya da bin doka da oda tare da bayar da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a lokutan bukukuwan Sallah da kuma bayan bikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp