DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata
Published: 29th, January 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Son haihuwar ’ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin al’ummomi daban-daban.
A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba.
Ko waɗanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ’ya’ya maza a kan ’ya’ya mata?
NAJERIYA A YAU: Dabarun Noma Don Samun Kuɗaɗen Shiga DAGA LARABA: Me Ya sa Matasa Ba sa Ɗaukar Koyarwa A Matsayin Sana’a?Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar ’ya’ya maza a kan ’ya’ya mata.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Haihuwa
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ‘Yan Banga A Edo Suka Yi Sanadin Kashe Matafiya Mafarauta 16 – Direban Motar
“Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban.
A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda ’yan banga suka tare su. Daga nan ne, shugaban ‘yan bangar ya fara yi wa direban tambayoyi game da kayan da ya dauko da kuma fasinjojin sa. Duk da gabatar da takardar sahalewar hanya amma shugaban ‘yan bangar ya nuna zargi kan mafarautan, musamman saboda makamansu da karnukan da su ke tare da su a cikin motar.
Saboda haka, “Shugaban ‘yan bangar bai amince da su ba ya bukaci su sauko. Da jama’a suka ga irin makamansu da karnuka, sai suka far mana,” in ji direban. “Shugaban ya shaida wa wadanda ke wurin cewa, mu masu garkuwa da mutane ne kuma ‘yan Boko Haram ne, sai suka fara dukanmu.”
Direban tare da wasu mutum biyu, an ce shugaban ‘yan bangar ne ya daure su a hannu tare da kai su ofishin ‘yansanda da ke kusa, inda ya shaida cewa, masu garkuwa da mutane ne ya kamo, lamarin da ya sa aka tsare su cikin gaggawa.
Direban ya bayyana cewa, “A lokacin da aka sake mu na koma wurin, an riga an kashe mutane 16.”
Sai dai ya yi watsi da zargin cewa, lamarin rikicin kabilanci ne. “Wannan ba rikicin kabilanci ba ne, ‘yan banga ne kawai ke da alhakin wannan harin, su ne suka sa aka kashe mutanenmu cikin ruwan sanyi,” in ji shi.
Wannan mummunan lamari dai ya janyo tofin Allah tsine a fadin kasar, tare da yin kira da a gudanar da cikakken bincike domin hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp