Tinubu Ya Yi Alƙawarin Inganta Wutar Lantarki A Nijeriya
Published: 29th, January 2025 GMT
Tinubu ya gode wa shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, saboda ƙoƙarinsu na samar da karin wutar lantarki a Afirka.
Ya kuma ce yadda masu zuba jari ke gamsuwa da shirye-shiryen gwamnatinsa ya sa aka samu jarin dala biliyan shida a ɓangaren samar da makamashi a shekarar da ta gabata.
Hukumar IFC ta sanar da cewa za ta saka dala miliyan 70 domin taimaka wa ‘yan kasuwa su samar da wutar lantarki ta hanyoyin da ba sa gurɓata muhalli.
Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na buƙatar aƙalla dala biliyan 23.2 domin inganta ɓangaren wutar lantarki da tabbatar da wadatarta ga al’umma.
Taron ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da dama, ciki har da shugabannin Afirka ta Kudu, Ghana, Rwanda, Tanzania, da kuma mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed.
Sauran mahalarta sun haɗa da shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.
কীওয়ার্ড: Alƙawari Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Fafaroma Frasncis ya rasu yana da shekaru 88
Allah Ya yi wa Shugaban mabiya ɗarikar Katolika na duniya, Fafaroma Frasncis, rasuwa yana da shekaru 88.
Fadar Vatican ce ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis a safiyar Litinin a yayin da al’ummar Kirista na duniya ke bikin Ista.
Ya mutu ne washegari da ya fito bainar jama’a a Dandalin St Peter’s, domin taya Kiristoci murnar zagayowar ranar Ista.
A watan da ya gabata ne aka sallame daga asibiti bayan ya yi jinya na tsawon makonni biyar.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron shi ne na farko wajen mika sakon ta’aziyya a cikin shugabannin duniya.