Kiristoci sun yi addu’ar ɗorewar zaman lafiya a Kudancin Kaduna
Published: 29th, January 2025 GMT
Ƙungiyar Shugabannin Kiristoci na Kudancin Kaduna (SKCLA) ta yi kira ga al’ummar yankin da su rungumi haɗin kai da ƙaunar juna a matsayin tubalin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba.
Shugaban ƙungiyar SKCLA, Fasto Emmanuel Nuhu Kure ne ya yi wannan kiran ga mazauna yankin a wajen taron addu’ar shekara-shekara da ake gudanarwa a garin Kafanchan don kyautata alaƙarsu da Ubangiji tare neman ɗauki daga gare Shi don samun zaman lafiya da wadata.
“Lokaci ya yi da za mu haɗa kai da tunanin mu waje ɗaya da manufa ɗaya don sake gina al’ummomin Kudancin Kaduna,” inji Kure.
“Dole ne mu koyi son makwabtanmu musulmai ba tare da wariya ba. Idan har babu haɗin kai, ba za mu samu makoma mai kyau ba.”
Malamin ya jaddada buƙatar sake gina yankin inda ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da ta jiha kan inganta tsaro a yankin.
“A cikin shekaru biyu da suka gabata zamu iya cewa mun samu zaman lafiya, yanzu za mu iya numfasawa da kyau kuma mu yi barci idanunmu biyu a rufe, muna jin daɗin zaman lafiyar da ke gudana,” inji shi.
Kure ya kuma yi kira ga manyan mutane daga Kudancin Kaduna da su yi amfani da wannan damar na zaman lafiya wajen kafa masana’antu da za su samar da aikin yi ga matasan yankin ba tare da jiran gwamnati sai ta yi komai ba.
Babban baƙo mai jawabi, Bishop Zakka Nyam na Cocin Anglikan da ke Kano, ya bayyana fatansa na kasancewar shekara 2025 da ta zamo shekarar sauyi ga Kudancin Kaduna.
Ya ce lokaci ya yi da jama’ar yankin za su yi watsi da dabi’ar yawaita gine-ginen Otal a yankin maimakon haka su fara gina masana’antu don sarrafa abubuwan da ake nomawa a yankin.
A nasa jawabin, Mataimakin Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Kaduna, Hon. Henry Magaji Danjuma ya bayyana yankin Kudancin Kaduna a matsayin yanki mai yalwar albarkatu, tare da yin kira ga mazauna yankin da su mara wa gwamnatinsu baya don samun ƙarin romon dimokuraɗiyya.
An gudanar da addu’o’i da waƙe-waƙen ibada musamman don ceto yankin, da Jihar Kaduna da kuma ƙasar baki ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna ya dakatar da basarake kan satar mutane da yankinsa
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da basaraken yankin Masarautar Uwano Kingdom, Dakta George Oshiapi Egabor, nan take saboda matsalar yi garkuwa da mutane a yankin.
Dakta George Oshiapi Egabor shi ne Okumagbe na Masarautar Uwano da ke Agenebode a Karamar Hukumar Etsako ta jihar.
Kakakin gwamnan, Fred Itua, a cikin wata sanarwa, ya bayyana cewa an dakatar da basaraken ne har sai abin da hali ya yi, saboda yawan samun kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane a masarautarsa a baya-bayan nan.
Ya ce tuni jami’an tsaro suka tsare sakataren basaraken, Cif Peter Omiogbemhi, sakamakon wani sabon hari a da ya yi ajalin wani bafade, Cif John Ikhamate. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 An tsinci gawar saurayi da buduwarsa a tuɓe a cikin daƙi A baya-bayan nan an samu yawaitar garkuwa da mutane a yankin, wanda ya haddasa ƙone ofishin ’yan sandan da ke kula da yankin. Daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su har da wasu malaman coci guda uku da aka yi aka yi awon gaba da su a wani coci, inda daga baya aka sako biyu bayan an biya kudin fansa, na ukun kuma aka kashe.