Masu Zanga-zanga Sun Farmawa Ofisoshin Jakadancin Amurka Da Na Faransa A DR Congo
Published: 29th, January 2025 GMT
Masu zanga-zanga sun kai hari kan ofisoshin jakadancin kasashen waje da dama hari a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo (DRC).
An bayar da rahoton cewa, fusatattun masu zanga-zangar sun kai wa ofisoshin jakadancin Amurka, Faransa, Belgium, Rwanda, Uganda, Kenya da Afirka ta Kudu hari.
Masu zanga-zangar dai na neman hadin kan kasashen waje da yunkurin kasa da kasa na shiga tsakani na soji da kuma dakatar da ‘yan tawayen M23 da ke ci gaba da mamaye wasu sassan yankin gabashi.
‘Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa amma masu zanga-zangar sun samu damar shiga sassan harabar, inda suka yi banka wuta.
Rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi da kungiyar ta M23 ya yi Kamari a baya bayan nan, inda suka kwace iko da Goma babban birnin gabashin Congo, ko da yake rundunar sojin Congon ta ce har yanzu tana iko da kashi 80 na birnin.
Masu zanga-zangar a Kinshasa sun bukaci kasashen duniya su matsa lamba kan kasar Rwanda kan ci gaban da dakarun ‘yan tawayen suka yi.
Tashin hankali a yankin da ake fama da rikicin kabilanci ya haifar da daya daga cikin manyan matsalolin jin kai a duniya.
A shekara ta 2012, ‘yan tawayen M23 sun mamaye birnin na Goma na wani dan lokaci kafin a tilasta musu janye dakarunsu a karkashin matsin lamba daga kasashen duniya.
A shekara ta 2021, dakarun ‘yan tawayen sun sake haduwa bisa tallafin da suke samu daga kasar Rwanda, a cewar gwamnatin Kinshasa da kwararrun MDD, saidai gwamnatin Kigali na mai musanta hakan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Masu zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa : An kama wata ‘yar Iran mai goyon bayan Falasdinu
A faransa ana ci gaba da tsare wata ‘yar Iran mai goyan bayan Falasdinu, bis azarginta da iza ta’addanci.
Mahdieh Esfandiari (mai shekaru 35) ana tsare da ita tun ranar 28 ga watan Fabrairu, bayan kama ta a binrin Lyon, inda ta ke da zama.
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ya yi Allah wadai da kama Mahdieh Esfandiari, yana mai yin Allah wadai da “manufofin kasashen Turai” wanda “ya kunshi murde adawa da “kisan kare dangi” da Isra’ila ta yi a Gaza.
Ya kara da cewa ba a sanar da ofishin jakadancin Iran da ke birnin Paris da kuma iyalan yarinyar ba.
A nasa bangaren, lauyan Mahdieh Esfandiari, Nabil Boudi, ya nuna rashin jin dadinsa kan kamun da aka yi wa wadda yake karewa.