Iran Ta Yi Watsi Da Shirin Trump Na Tilastawa ‘Yan Gaza Barin Yankinsu
Published: 29th, January 2025 GMT
Iran ta mayar da martani game da shirin shugaban kasar Amurka Donald Trump na tilastawa Falasdinawan Gaza komawa kasashen Jordan da kuma Masar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmaeil Baghaei ya yi watsi da shirin na Trump a wani sako a kan shafinsa na X.
Baghaei ya ce, kisan kiyashin da gwamnatin Isra’ila ta kwashe watanni 15 tana yi, ya kasa kawar da Falasdinawa daga tushensu, don haka ba wani abunda zai iya tilasta musu ficewa daga yankinsu.
“Wannan ita ce kasarsu ta asali kuma sun sadaukar da komi don su ci gaba da zama a can kuma su ci gaba da gwagwarmayar neman yancin kai,” a cewar kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran.
Wannan kiran na Trump dai ya zo ne duk da tsananin adawar da Alkahira da Amman suka bayyana wa shirin da ya bayyana da na tsaftace yankin Gaza.
Shi dai Trump ya yi ikirarin cewa matakin na iya “kawo zaman lafiya” a yammacin Asiya idan Masar, Jordan, da sauran kasashen Larabawa suka karbi ‘yan gudun hijirar Falasdinu.
Trump ya ce tuni ya tattauna da Sarki Abdallah na biyu na Jordon kan yiwuwar gina gidaje da kuma kwashe Falasdinawa sama da miliyan daya daga Gaza.
Alkahira da Amman sun yi watsi da shawarar Trump a hukumance.
Manazarta sun ce duk wani shiri na tsugunar da Falasdinawan da suka rasa matsugunnai, zai bai wa gwamnatin Isra’ila uzurin da ta ke bukata na korar al’ummar Gaza da karfi, da kuma sake mamaye yankin.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Watsi Da Zargin Takurawa Mataimakin Shugaban Kasa Shettima
Fadar shugaban kasa ta musanta rahotannin da ke nuni da cewa an hana mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, GCON shiga fadar shugaban kasa, inda ta bayyana ikirarin a matsayin shirme, kage da kuma karya gaba daya.
Wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da sadarwa na ofishin mataimakin shugaban kasa Stanley Nkwocha ya sanyawa hannu, ta ce rahoton da wasu shafukan da ba su da tushe suka yada shi, na cikin jerin labaran karya da aka kitsa domin haifar da rashin jituwa tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa.
Sanarwar ta kara da cewa, “Wannan wani yunkuri ne mai rauni na cin mutuncin mutum da ofishin Mai Girma, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima.
Nkwocha ya ce labarin da ake cewa sojoji dauke da makamai sun hana mataimakin shugaban kasa shiga fadar Shugaban kasa wato Villa ba wai kawai an yi ne ba haka kawai, a’a har ma ya nuna rashin fahimtar ayyukan gwamnati.
Sanarwar ta ce, wannan shi ne mafi girman furuci na fatar baka, kuma hakan yana nuni da cewa masu yin wannan tatsuniyoyi sun gaji da zargi da kuma hasashe, in ji sanarwar.
Wannan dai ba shi ne karon farko da fadar shugaban kasar ke yin watsi da irin wadannan rahotannin ba. Kwanaki kadan kafin hakan, ta karyata labaran karya da ke yawo a shafukan yakin neman zabe dauke da hoton shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu. Fadar shugaban kasar ta yi imanin cewa irin wannan karyar wani yunkuri ne na kawo cikas ga hadin kai da amincin shugabancin kasar.
Mataimakin shugaban kasar ya ci gaba da maida hankali kan ayyukan sa da kuma marawa shugaban kasar baya wajen cimma muradun ‘yan Najeriya. Sanarwar ta kara da cewa, ba shi da wani abin da zai raba hankali.
Nkwocha ya yabawa ‘yan Najeriya da ke ci gaba da nuna goyon bayansu ga gwamnatin Tinubu-Shettima, ya kuma bukaci kafafen yada labarai da su nemi bayanai daga majiyoyi masu inganci tare da yin taka-tsan-tsan wajen bayar da rahotanni masu ban sha’awa.
Sanarwar ta kara da cewa, “alkwarin da ke tsakanin wannan gwamnati da ‘yan Najeriya ya yiwu ne ta hanyar halaltaccen tsarin mulki.
Bello Wakili