Ademola Lookman Ba Zai Buga Wasan Atalanta Da Barcelona Ba
Published: 29th, January 2025 GMT
Ɗan wasan Nijeriya kuma gwarzon ɗan ƙwallon ƙafar Afrika, Ademola Lookman, ba zai buga wasan da Atalanta za ta kara da Barcelona a gasar cin kofin Zakarun Turai yau Laraba ba, sakamakon rauni da ya ji a gwiwarsa.
A wata sanarwa da kulob ɗin Atalanta ya fitar, ya ce ɗan wasan mai shekaru 27 ya samu rauni a gwiwar dama a lokacin atisayen safiyar Talata, wanda ya hana shi tafiya Spain don buga wasan da ƙungiyarsa ke neman cancantar shiga zagayen 16 na ƙarshe.
Duk da cewa kulob ɗin bai bayyana tsawon lokacin da Lookman zai yi jinya ba, kafofin labarai a Italiya sun ruwaito cewa zai ɗauki kusan wata guda kafin ya dawo.
Lookman dai babban rashi ne ga Atalanta, duba da cewa ya zura ƙwallaye 14 tare da bayar da taimako a ƙwallaye shida a wannan kakar wasa.
এছাড়াও পড়ুন:
Babu Wata Suka Da Za Ta Hana Gwamna Dauda Lawal Aiwatar da Ayyuka.
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa babu wani kamfen batanci da zai hana Gwamna Dauda Lawal aiwatar da ayyukan da suka shafi al’umma a fadin jihar.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da sadarwa na gwamna, Malam Salihu Nuhu Anka ya rabawa manema labarai a Gusau.
A cewar Anka, Gwamna Lawal ya fara aiki ne a wani aikin ceto, kuma tuni mazauna jihar suka fara cin ribar dimokuradiyya.
Ya bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne kan kalaman da ya bayyana a matsayin maras tushe da wani tsohon Kwamishinan Yada Labarai, Ibrahim Magaji Dosara ya yi, yayin wani taron manema labarai a Kaduna, inda ya kalubalanci kalaman da Gwamna Lawal ya yi a wata hira da ya yi da shi kwanan nan.
“A yayin taron manema labarai, Dosara ya kai wa Gwamna Dauda Lawal hari cikin rashin kunya a kokarinsa na burge tsohon Gwamna Bello Matawalle,” Anka ya yi zargin.
REL/AMINU DALHATU.