Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA
Published: 29th, January 2025 GMT
Hukumar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi (NDLEA) reshen Jihar Yobe ta ce ta kama wasu haramtattun ƙwayoyi da nauyinsu ya kai kilo 537 tare da kama wasu mutum 46 da ake zargi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a shekarar 2024.
Kwamandan hukumar ta NDLEA a Jihar Yobe, Mista Abdulazeez Ogungboye ne ya bayyana hakan a Damaturu yayin da yake bitar ayyukan hukumar na shekara guda da ta gabata.
Ya ce magungunan da aka kama sun haɗa da kilo 396.526 na tabar wiwi da kilo 141.2 na sauran kayayyakin maye.
Ogunboye ya ce hukumar ta miƙa mutane 21 cikin mutane 46 da ake zargi da aikata laifukan a gaban kuliya domin yanke musu hukuncin da ya dace da su, yayin da ake ci gaba da shari’ar 85 a Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu.
Kwamandan ya ce hukumar ta bayar da shawarwari ga mutane 219 da suka dogara da muggan kwayoyi tare da gudanar da gangamin wayar da kan jama’a a cikin al’umma, makarantu, ƙungiyoyin addini, da wuraren aiki.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Jihar Yobe
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kebbi Za Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai A Saudiyya
Gwamnatin Jihar Kebbi ta kammala shirye-shiryen daukar nauyin dalibai 70 zuwa Masarautar Saudiyya domin karatun digiri a fannoni na addini da na zamani.
Wannan na daga cikin shirin “Kaura Capacity Building Project 2025“ karkashin ma’aikatar kula da harkokin addinai ta jihar.
A yayin wani taron manema labarai, mai bai wa Gwamna shawara kan harkokin addinali, Injiniya Imran bn Usman, ya bayyana cewa kowanne daga cikin kananan hukumomi 20 na jihar za su ba da sunayen dalibai uku, yayin da aka ware wa babban birnin jihar, Birnin Kebbi, guraben dalibai 10.
Ya bayyana cewa, gwamnatin jihar ce za ta dauki nauyin tafiyar daliban zuwa Saudiyya, yayin da gwamnatin Saudiyya za ta dauki nauyin karatunsu da walwalarsu bayan isarsu.
Mai ba da shawarar ya kara da cewa, ana sa ran kowacce karamar hukuma za ta gabatar da dalibai maza biyu da mace daya, don neman guraben karatun digiri a fannin addinin Musulunci ko sauran fannoni na zamani.
Ya kuma kara da cewa, an kammala shirin tura limaman masallatai Jumu’a zuwa kasashen waje domin horo na gajeren lokaci a fannin yadda ake gabatar da huduba da Hadisi, don kara inganta tasirinsu yayin gabatarda Sallah.
Daga Abdullahi Tukur