Aminiya:
2025-03-03@09:38:34 GMT

Jirgin Max Air ɗauke da fasinjoji 59 ya tsallake rijiya da baya a Kano

Published: 29th, January 2025 GMT

Wani jirgin kamfanin Max Air ya tsallake rijiya da baya yayin sauka a filin jirgin Malam Aminu Kano (MAKIA) a ranar Talata da daddare.

Jirgin wanda yake ɗauke da fasinjoji 53 da ma’aikata shida yana dawowa daga Jihar Legas ne lokacin da haɗarin ya faru.

Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Mun kama mutum 46 da miyagun ƙwayoyi a Yobe — NDLEA

Wani fasinja ya bayyana cewa jirgin ya rasa tayar gabansa yayin sauka a filin jirgin.

Fasinjan ya yi karin bayani da cewa cewa tayar jigin ta fashe sannan ta kama da wuta a daidai lokacin da ya sauka cikin filin da misalin karfe 10:19 na dare.

“Daidai lokacin da tayar ta taɓa ƙasa sai ta kama da wuta, hayaki ya turnuke a cikin jirgin wanda ya sa dole muka fita ta ƙofar fitar gaggawa.

“Yayin da muke fitowa daga jirgin, wasu ’yan kashe gobara sun riga sun fara watsa wa jirgin ruwa domin kashe wutar.”

Da yake zantawa da manema labarai, Manajan Max Air reshen Jihar Kano, Malam Bello Ramalan, ya ce ba a samu asarar rai ko jin rauni ba.

“Ina ba da haƙuri bisa matsalar da ta faru, kuma muna godiya ga Allah bisa tseratar da fasinjojin da Ya yi. Ni lafiyar fasinjoji ce a gabana.

“Dangane da bin dokokin saukar jiki, kamfaninmu ya bi ka’idojin da suka dace na yin saukar gaggawa, wanda Allah Ya sa abin ya zo da sauƙi.

“Ka’idojin sun hada da fitar da fasinjoji cikin gaggawa, killace matuƙa jirgin da kuma haɗa kai da hukumomin bincike.”

Kamfanin Max Air ya ce yana aiki tare da hukumar binciken haɗuran jiragen sama AIB da AED domin bincike kan dalilin aukuwar lamarin.

Malam Ramalan ya ce “bincike na farko ya nuna cewa matsalar tayar jirgin ce ta haddasa haɗarin.”

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha

Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya bayyana cewa matarsa ta taɓa kawo masa ƙorafi game da cin zarafin da ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi mata.

A cewarsa, rikicin ya fara tun lokacin da Natasha ta tsaya takarar kujerar Sanata a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, inda ta nemi kujerar Sanatan Kogi ta Tsakiya.

Mu ne muka kai samame otal ba ’yan bindiga ba — EFCC Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano

A lokacin, Akpabio yana riƙe da mukamin Ministan Neja Delta.

“Da kaina na je na same shi na buƙaci ya bai wa matata girman da ta cancanta, sannan ya girmama abotar da ke tsakaninmu.

“Bayan mun tattauna sai muka amince da a warware maganar cikin mutunci,” in ji shi.

Bayan zaɓen 2019, Natasha ta sake tsayawa takarar Sanata a 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP, inda ta samu nasara.

A lokacin, ana raɗe-raɗin cewa Akpabio bai ji daɗin yadda ta samu goyon baya ba, kuma hakan ya ƙara haddasa rashin jituwa a tsakaninsu.

“Amma bayan maganar da muka yi, sai matata ta ci gaba da bayyana damuwa game da irin cin zarafin da ta ke fuskanta daga shugaban majalisar.

“Ni dai na yarda da matata, kuma aure muka yi na soyayya da ƙauna. Babu abin da ya fi min ita a yanzu domin ita ce farin cikina.”

Natasha dai ta ce tana da wasu hujojji da za ta fitar, wanda ke nuna yadda Akpabio ya neme ta, lamarin da yanzu haka ya haifar da zazzafar muhawara a Najeriya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jagora: Iran Tana Fuskantar  Makiya Na Waje Kafirar Da Munafikai
  • Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya
  • Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha
  • Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Edo
  • Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • Ramadan: Ga arahar kayan abinci ga rashin kuɗin saya
  • Ka Cire Sarkin Kano Bayero Daga Fadar Nasarawa – Gwamnatin Kano Ga Tinubu
  • Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa
  • Dalilin Dakatar Da Shugaban Ma’aikatan jihar Kano