Aminiya:
2025-03-03@18:23:54 GMT

Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu

Published: 29th, January 2025 GMT

Wata matashiya mai shekaru 20 ta shiga hannun ‘yan sanda bisa zarginta da ƙona matar ɗan uwanta da ke naƙuda da tafasasshen ruwan zafi.

A tattaunawarta da Aminiya, matashiyar ta ce ɓacin rai ne ya kai ta ga ƙone matar lokacin da musu ya kaure a tsakaninsu.

Jirgin Max Air ɗauke da fasinjoji 59 ya tsallake rijiya da baya a Kano Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS?

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba a garin Dubeli da ke ƙaramar hukumar Yola ta Arewa da ke Jihar Adamawa.

Mijin matar da aka ƙona ya ce yana shago ne inda yake sana’a aka kira shi a waya cewa an watsa wa matarsa ruwan zafi lokacin da take naƙuda.

Kazalika ya nuna takaicinsa na sanin ‘yar uwarsa ce ta aikata ta’asar, kuma jim kaɗan bayan hakan ne matar tasa ta haihu.

A nasa ɓangaren, Kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nguroje ya tabbatar da kama matashiyar da ake zargin, ya kuma ce za su ci gaba da bincike kafin miƙa ta kotu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Matashiya Ruwan zafi

এছাড়াও পড়ুন:

Noman Rani: Tinubu Ya Amince Da Fadada Madatsun Ruwa 12 A Nijeriya

Ya yi nuni da cewa, wannan amincewa ta Shugaban Kwamitin; daidai take da irin manufar Shugaban Kasa Tinubu, ta son kara bunkasa kasar nan kafin zuwan zabukan 2027.

Kwankwaso ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, kan irin hangen nesansa, musamman wajen mayar da hankali kan samar da wadataccen abinci da kuma kokarin sake farfado da tattalin arzikin kasar.

Kazalika, ya yaba wa Shugaban Kwamtin kan gundunmawar da ya bayar wajen gainin an samar da wadannan ayyuka.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • CMG Zai Watsa Bikin Bude Zama Na Uku Na Majalisar CPPCC Karo Na 14
  • Jagora: Iran Tana Fuskantar  Makiya Na Waje Kafirar Da Munafikai
  • Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio — Mijin Natasha
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • Kamfanoni 10 Sun Zuba Jarin $466m A Jihar Nasarawa
  • Shugaban Kasar Ukraine Ya Sami Tarba Mai Kyau A Burtaniya Bayan Cacan Baki Mai Zafi Da Trump
  • Gobara Ta Sake Ƙona Kasuwar Kara A Sokoto
  • Abubuwan Sha Domin Karin Ni’ima Ga Mata
  • Noman Rani: Tinubu Ya Amince Da Fadada Madatsun Ruwa 12 A Nijeriya
  • Kwastam Da Hukumar NPA Sun Kulla Hadakar Bunkasa Ingancin Aiki A Tashoshin Jiragen Ruwa