Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici
Published: 29th, January 2025 GMT
Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar.
Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa.
Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS?Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun.
A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu.
Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma.
Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don tsayawa takarar Gwamnan Jihar Imo, takarar da bai yi nasara ba.
A lokacin da ba ya nan, ɓangaren jam’iyyar na Kudu maso Gabas ya naɗa Ude-Okoye a matsayin sabon sakataren jam’iyyar.
Amma bayan Anyanwu ya faɗi a zaɓen gwamna, ya yi ƙoƙarin karɓe kujerarsa a jam’iyyar, wanda hakan ya haddasa rikici.
A ranar 20 ga watan Disamban 2024, kotun ɗaukaka ƙara da ke Enugu ta tabbatar da hukuncin wata babbar kotu da ta tuɓe Anyanwu daga kujerar sakataren jam’iyyar, tare da tabbatar da Ude-Okoye a matsayin halastaccen sakatare.
Anyanwu ya ɗaukaka ƙara tare da neman dakatar da hukuncin.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Sakatare Sakatariya
এছাড়াও পড়ুন:
Hotunan Sallar Idi daga sassan duniya
Miliyoyin Musulmi ne a faɗin duniya ke bikin Ƙaramar Sallah bayan kammala azumin Ramadana.
Ku ci gaba da kasancewa da shafin Aminiya domin samun hotunan yadda aka gudanar da Sallar Idi a wasu sassan duniya da kuma nan gida Nijeriya.