Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka
Published: 29th, January 2025 GMT
Sama da ’yan Najeriya 5,000 da ke zaune a Amurka ba bisa ƙa’ida ba, na fuskantar barazanar dawo da su gida.
Daga cikinsu, kusan 1,500 ne ake tsare da su, wanda hakan na daga cikin matakin da sabon Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ɗauka na korar baƙin haure da masu neman mafaka ba bisa ƙa’ida ba.
Jami’an tsaro sun mamaye sakatariyar PDP bayan ɓarkewar rikici Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS?Alƙaluman da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Amurka (ICE), ta fitar a watan Nuwamban 2024, sun nuna cewa akwai mutum miliyan 1.
Sai dai sabbin alƙaluman da ICE ta sake fitarwa, sun nuna cewa an ƙara samun wasu mutum 1,454 daga Najeriya da ake tsare da su, kuma ana shirin dawo da su gida.
Hukumar ta ce daga cikin waɗanda ake tsare da su, 772 na jiran hukunci, yayin da aka riga an yanke wa wasu hukunci saboda laifuka daban-daban, ciki har da na karya dokokin shige da fice.
Duk da cewa Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.
Sai dai hukumar da ke kula da ’yan Najeriya a ƙasashen waje ta ce ta kafa wani kwamiti da zai binciki matsalar tare da duba hanyoyin da za a bi domin magance ta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Burnley Da Leeds United Sun Dawo Gasar Firimiya Lig
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Burnley United tare da takwararta ta Leeds United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya bayan samun nasara a mabanbantan wasannin da suka buga.
Burnley ta doke Sheffield United da ci 2-1 da yammacin yau domin samun wannan nasarar, hakazalika Leeds United ta samu nasara akan Stoke City da ci 6-0 a daya wasan na yau, dukkan kungiyoyin biyu zasu buga gasar Firimiya Lig ta badi.
Alex Iwobi Ya Kafa Tarihi A Gasar Firimiya Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar FirimiyaYayinda kungiyoyin Firimiya Southampton da Leicester City suka koma gasar Championship su kuma Burnley da Leeds United sun samu nasarar tsallakawa zuwa gasar Firimiya a kakar wasa ta badi.
Yanzu za a jira daya kungiyar daga Championship domin sanin wadanda zasu buga gasar Firimiya a badi, hakazalika za a jira kungiya daya da zata koma gasar yan dagaji daga Firimiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp