Alkaluman Watsa Shirye-Shiryen Shagalin Bikin Bazara Na CMG Na 2025 Sun Kai Sabon Matsayi
Published: 29th, January 2025 GMT
Shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na shekarar 2025 sun gabatar da wata “liyafar al’adu” mai kyau da ban sha’awa, kuma mai fasahohi ga masu kallo na gida da waje, bisa sabbin dabaru. Ya zuwa karfe 2 na sanyin safiyar yau Laraba, a dukkan kafafen yada labarai, yawan mutanen da suka kalli shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG ya kai sau biliyan 16.
Bugu da kari, yawan masu kallon shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 ta hanyar talabijin yayin da aka watsa shi kai tsaye a cikin kasar, ya kai kashi 78.88 cikin dari, wanda ya kafa sabon tarihi a cikin shekaru 12 da suka gabata.
Ban da haka, an tattauna shirye-shiryen shagalin bikin bazara na CMG na 2025 har sau biliyan 27 a dandalolin sada zumunta a kasar Sin, adadin da ya zarce na bara.(Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Babu dokar da na karya saboda yin taron a mazaɓata — Natasha
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin jihar ta yi ba karya doka ba ne.
Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda dalilin da ta ce na tsaro ne.
Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da SallahKwamishinan ‘Yan sandan jihar, Miller Ɗantawaye, ya ce hana taron ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu cewa za a samu barzanar tsaro, wanda ya tilasta gwamnatin jihar ɗaukar matakin.
Sai dai Natasha wadda ta isa jihar a wani jirgi mai saukar ungulu, ta bayyana wa magoya bayanta cewa tana da ’yancin kasancewa da mutanenta ta kuma yi shagalin farin ciki tare da su.
“A duk abin da za mu yi, mu sanya Allah a farko kuma mu shigar masa da buƙatunmu ta hanyar addu’a.
“Mijina ya kasance ɗaya daga cikin addu’o’ina da Allah Ya amsa. In banda haka ta yaya ni da ba kowa ba ce fa ce talaka daga ƙabilar Ebira na samu ƙarfin samun jirgin da zai kawo ni gida?
“Goyon bayan mijina ne ya kawo haka, kuma shi ke ciyar da ni gaba a koda yaushe.
“Tun jiya da na samu labarin za a rufe hanyoyi, aka kuma haramta taruka da jerin gwanon motoci a cikin gari na san cewa mu ne ake so a muzgunawa.
“Amma sai na faɗa wa kaina ai ba kakar siyasa ko yaƙin neman zaɓe ba ne yanzu.
“Don haka ni ba yaƙin neman zaɓe zan yi ba. Ni kaɗai ce zan shigo gari cikin mutane na, na yi shagalin bikin Sallah tare da su.
“Don haka babu wani laifi a ciki, babu dokar da na karya. A Najeriya muke. Ina da ’yancin shiga taruka da bukukuwa.