‘Yan Tawayen M23 Sun Kara Shimfida Ikonsu A Garin Goma
Published: 29th, January 2025 GMT
Kungiyar M 23 da take samun goyon bayan Rwanda tana kara karfafa ikonta a garin Goma dake gabashin jamhuriyar Demokradiyyar Congo, da su ka hada da filin saukar jiragen sama, kamar yadda MDD ta sanar.
A yau Laraba shugaban kasar Rwanda da gwmanatinsa take goyon bayan ‘yan tawayen kungiyar M23, ya yi kira da a tsagaita wutar yaki.
Da safiyar yau Laraba an sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Goma bayan da a jiya mazaunansa fiye da miliyan biyu su ka kasance a cikin zullumi da fargaba.
Mazauna birnin na Goma sun fadawa kamfanin dillancin Labarun (AP) cewa ‘yan tawayen kungiyar ta M 23 ne suke rike da mafi yawancin birnin.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai kungiyar ta M 23 ta sanar da cewa ta kame wannan birnin na Goma bayan mayakanta suka dauki kusan mako daya suna matsawa kusa da shi.
Kungiyar M 23 daya ce daga cikin kungiyoyin tawaye 100 da ake da su a cikin kasar ta jamhuriyar Demokradiyyar Congo da kowace daya daga cikinsu take son shimfida iko a cikin yankunan da ake da ma’adanai.
Ita dai kasar DRC tana da dimbin arzikin ma’adanai da suke kwance a karkashin kasarta, da ya sa kasashen makwabta da kuma na nesa suke taimakawa wasu daga cikin kungiyoyin ‘yan tawaye saboda su yi kaso mu raba da arzikin wannan kasar.
Tun da kasar ta Sami ‘yanci daga kasar Belgium, ba ta sami zaman lafiya ba har zuwa yanzu.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Masar Ta Tabbatrawa Falasdinawa, Tana Bayansu Kafin Taron Kasashe Larabawa
Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira.
Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa.
Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967.
A ranar Talata 4 ga watan Maris da muke ciki ne za’a gudanar da taron gaggawa na kungiyar kasashen larabawa a birnin Alkahira na kasar Masar don tattauna halin da Falasdinawa suke ciki musamman a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan.