Sojojin Sudan Sun Kwance Iko Da Garin “Khartum-al-Bahri”
Published: 29th, January 2025 GMT
A yau Laraba ne dai sojojin Sudan su ka sanar da shimfida ikonsu a garin ‘Khartum-al-Bahri.
Majiyar sojan kasar ta Sudan ta kuma bayyana cewa, a halin yanzu suna aiki tare da bangarorin da suke dace, domin ganin fararen hula mazauna garin sun koma gidajensu a cikin lokaci mafi kusa.
A cikin kwanaki kadan da su ka gabata sojojin na kasar Sudan sun sami nasarar kwace yankuna da dama a kewayen Khartum-al-Bahri da su ka hada da gabashin tekun maliya.
Wannan cigaban da sojojin na Sudan su ka samu, ya biyo bayan korar dakarun rundunar kai daukin gaggawa ne daga babbar shalkwatar soja dake tsakiyar birnin Khartum, haka nan kuma cibiyar sojan ta sadarwa, da babbar cibiyar leken asiri ta soja dake kusa da Khartum-al-Bahri.
A wata sanawar ta daban da sojojin kasar ta Sudan su ka fitar sun bayyana cewa jiragen yaki sun kai hare-hare a garin al-Fashar da can ne babban birnin yankin Darfur. Wannan yankin shi ne babban sansanin mayakan dakarun rundunar kai daukin gaggawa.
Sojojin na Sudan sun ce, sun kai wadannan hare-haren ne dai da safiyar Yau Laraba.
A wani labarin daga Sudan, rundunar kai daukin gaggawa ta sanar da cewa, an kashe daga cikin kwamandojinta mai suna Rahmatullah al-Mahadi wanda aka fi sani da Jalha a jiya Talata, ba tare da bayyana yadda aka kashe shi din ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Khartum al Bahri
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Masallacin Juma’a A Garin Samamiya Da Ke Birnin Kudu
Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce za ta duba yiwuwar inganta cibiyar lafiya tare da kafa makarantar sakandare a garin Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu.
Gwamna Umar Namadi ya bayyana haka a lokacin kaddamar da sabon masallacin Juma’a da gidan marayu da makarantar islamiyya, wanda dan asalin yankin Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya ya gina a matsayin wakafi ga mahaifinsa.
Malam Umar Namadi ya bayyana jin dadinsa bisa wannan kokari na Alhaji Muhammad Abubakar Samamiya.
Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da su yi koyi da wannan matakin domin amfanin talakawa da marasa galihu a cikin al’umma.
Ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin aiki kafada da kafada da irin wadannan mutane a cikin al’umma.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, Gwamna Umar Namadi tare da rakiyar sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim, da ‘yan majalisar zartarwa na jiha, da shugaban karamar hukumar Birnin Kudu da sauran manyan baki sun yi sallar Juma’a a sabon masallacin Abubakar Samamiya da ke karamar hukumar Birnin Kudu.
Usman Muhammad Zaria