Yahudawan Sahayoniya Suna Yin Hijirar Daga Haramtacciyar Kasar Isra’ila Zuwa Kasashen Waje
Published: 29th, January 2025 GMT
Jaridar “Le Monde” ta kasar Faransa ta dauki labarin da yake cewa iyalai masu yawa sun fice daga HKI baki daya zuwa kasashen Portugal,Cyprus, da kuma Girka.
Rahoton ya ci gaba da cewa; Dalilan yin hijirar daga HKI zuwa kasashen waje sun kunshi yaki, rashin tsaro da kuma siyasar gwamnatin Benjemine Netanyahu.
Har ila yau, jaridar ta kasar Faransa ta ce, dubban ‘yan share wuri zauna ne suke ficewa daga Falasdinu dake karkashin mamaya a wasu lokutan iyalai ne kaco kau suke ficewa.
Kwanaki kadan da su ka gabata wasu iyalai da suke kunshe da mutane 20 da su ka hada iyaye, kakanni da jikoki sun yi hijira zuwa Cyprus domin su rayu a can.
A cikin kafafen sadarwa na al’umma da akwai ‘yan share wuri zauna da dama da suke yin kira da a fice daga HKI zuwa kasashen Girka, Canada da Thailand domin ci gaba da rayuwa a can.
Batun yin hijirar ‘yan sahayoniya daga HKI ya fara ne tun farkon farmakin Guguwar Aksa, da suke komawa zuwa kasashen turai mabanbanta bayan da su ka tabbatar da cewa, rayuwarsu ba za ta dawwama ba a cikin kasar da su ka kwace daga masu ita na asali.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: zuwa kasashen
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Da Haddiyar Daular Larabawa Sun Gudanar Da Taron Kwamitin Siyasa Da Al-adu Na Kasashen Biyu
Kasashen Iran da Hadaddiyar Daular Larabawa sun gudanar da taron kwamitin Siyasa da al-adun na kasashen biyu a karon farko a birnin Abu Dhabi wanda ya kara tabbatar da irin ci gaban da suke samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kyautata dangantaka tsakanin kasashe makobta na daga cikin manufofin JMI ta harkokin wakashen waje.
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran Majid Takht-e Ravanchi ya bayyana cewa karfafa dangantaka da Hadaddiyar Daular Larabawa yana daga cikin manufofin JMI don biyan bukatun ko wace kasa daga cikin kasashen biyu.
Ya kuma kara da cewa akwai bukatar kasashen musulmi su kara hadin kai a tsakaninsu don magance matsalar da Falasdinawa suke fuskanta a hannun HKI da kuma kasashen yamma.