Yankin Gabashin Kongo(Kinshasa) Yana Cikin Yanayi Mai Hadari
Published: 29th, January 2025 GMT
Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron gaggawa game da batun Kongo(Kinshasa) da kwamitin sulhu ya kira jiya Talata cewa, a halin yanzu, yankin gabashin Kongo(Kinshasa) yana cikin yanayi mai hadari. Ya ce Sin na goyon bayan mambobin kwamitin sulhu su hada kai tare da daukar kwararan matakai, ta yadda za a samar da dabarun hana yanayin ya ci gaba da tsanani da kuma inganta warware batun a siyasance.
Fu Cong ya bayyana cewa, kwanan nan, yanayin Kongo(Kinshasa) ya shiga matsanancin yanayi ciki sauri, inda kungiyar M23 ta kai hari birnin Goma, hedkwatar jihar Kivu ta arewa dake kasar, lamarin da ya sanya fararen hula da yawa barin gidajensu, inda kuma hadarin barkewar rikici mai girma ke karuwa, wanda ke zaman abun damuwa matuka.
Ya nanata cewa, Sin za ta dage wajen goyon bayan ikon mulkin Kongo(Kinshasa) da mallakar cikakkun yankunanta, kuma tana adawa da dukkanin abubuwan dake keta tsarin dokokin MDD da dokokin kasa da kasa. Haka zalika, bangaren Sin yana bukatar kungiyar M23 ta daina dukkanin ayyukan nuna adawa, kuma ta janye daga yankunan da ta mamaye, kamar Goma.
Fu Cong ya kara da cewa, bangaren Sin yana tir da harin M23 kan ma’aikatan wanzar da zaman lafiya na MDD, kuma yana goyon bayan tawagar MDD dake Kongo(Kinshasa) ta gudanar da ayyukan kare fararen hula, karkashin amincewar kwamitin sulhun. Ya kuma jadadda cewa, babu wata hanyar bude wuta da za ta magance batun gabashin Kongo (Kinshasa), tattaunawa ta diflomasiyya ce kawai mafita. (Safiyah Ma)
এছাড়াও পড়ুন:
Sudan ta katse hulda da Hadaddiyar Daular Larabawa bisa goyon bayan dakarun RSF
Gwamnatin Sudan ta katse dangantakar diflomasiyya da (UAE), bisa zarginta da goyan bayan dakarun RSF.
A cikin jawabin da aka watsa a talabijin, Ministan Tsaron Sudan, Yassin Ibrahim ya bayyana cewa Sudan ta “katse dangantakar diflomasiyya da UAE,” tare da janye jakadanta da rufe ofishin jakadanci da konsulat dinta a kasar .
Da yake magana a gidan talabijin na gwamnatin kasa, ministan tsaron Sudan, Yassin Ibrahim Yassin, ya zargi Abu Dhabi da keta hurumin ‘yancin Sudan ta hanyar mara baya ta fuskar soji ga RSF, ciki har da samar da makamai, da jiragen yaki marasa matuka, da makamai masu linzami wadanda aka kai hari da su a baya-bayan nan a tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da kuma tashoshin wutar lantarki na Sudan.