EFCC ta cafke tsohon shugaban NHIS, Usman Yusuf a Abuja
Published: 30th, January 2025 GMT
Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun cafke Tsohon Shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIS), Farfesa Usman Yusuf, bayan kai sumame a gidansa da ke Abuja.
Aminiya ta tabbatar da cewa jami’an EFCC ɗauke da makamai sun isa gidansa da misalin ƙarfe 4:46 na yammacin ranar Laraba, inda suka kama shi a gaban matarsa da ’ya’yansa.
Sai dai har yanzu ba su bayyana dalilin cafke shi ba.
Wata majiya ta bayyana cewa an kama tare da tafiya da Farfesa Yusuf zuwa wani waje da ba a bayyana ba.
Duk da cewa hukumomi ba su fitar da sanarwa kan tuhumar da ake yi masa ba, wasu majiyoyi sun ce kamun nasa yana da alaƙa da shugabancin da ya yi a hukumar NHIS.
Wani babban jami’in EFCC ya ce, “Ba za a iya bayyana dalilin kama shi a yanzu ba saboda har yanzu ana bincike.
“Amma yana hannunmu kuma zai taimaka wajen gudanar da bincike.”
An cire Yusuf daga muƙaminsa a shekarar 2019 a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari.
Wani kwamitin bincike na Ma’aikatar Lafiya ne, ya bayar da shawarar korarsa bisa zargin ɓatan-dabon Naira miliyan 919.
Da aka tuntuɓi kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ce zai bincika batun sannan ya yi ƙarin haske daga baya.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai yi martani ba.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki.
Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi.
Burina in yi fice kamar mahaifiyata — Maryam ‘Yar Auta Abubuwan da ya kamata a sani game da azumin watan RamadanaKakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce, “saɓani ne ya kaure tsakanin wani mai suna Nuru Isah mai shekara 50 da matarsa ta biyu, Wasila Abdullahi kan tsarin abinci da kayan buɗa-baki na gidan.”
’Yan sanda sun ce bincike farko na nuna cewa mijin ya yi amfani da bulala wajen bugun matar mai shekaru 24, “inda ta yanke jiki ta faɗi, da aka kai ta asibitin koyarwa na jami’ar Tafawa Ɓalewa ne likitoci suka tabbatar da rasuwarta.”
Sanarwar ta ƙara da cewa ’yan sanda sun kama mijin, sun ɗauko bulalar da aka yi amfani da ita, sannan kuma za a yi binciken ƙwaƙwaf a kan gawar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Auwal Musa Muhammad, ya bayyana cewa za a gudanar da bincike domin tabbatar da adalci a lamarin.