Gwamnatin Kebbl Ta Dage Bikin Kamun Kifi Karo Na 61 Na Argungu Har zuwa Shekarar 2026
Published: 30th, January 2025 GMT
Ya kara da cewa, “a halin yanzu ,ana gudanar da aikin shimfida tagwayen hanyoyi a cikin tsakiyar garin Argungu da sauran wasu ayyukan ci gaba a masarautar. Saboda haka, wannan wata dama ce na kara shirye-shirye don tarbar baki da ke zuwa kallon shirin daga cikin gida da ketare. Wannan al’ada ce fitacciya a masarautar Argungu.
“Muna godiya da fahimta da hadin gwiwar masu ruwa da tsaki, da mahalarta wannan biki,” in ji Mataimakin Gwamnan jihar Kebbl Sanata Abubakar Umar Tafida.
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Gargadi Malaman Da Ba Sa Zuwa Aiki
Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa zuwa aiki.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin.
A cewarsa, wani bincike da aka gudanar bayan hawansa karagar mulki, ya nuna cewa malaman makarantu da dama ba kasafai suke zuwa aiki ba.
Ya ce hakan na daga cikin dalilan tabarbarewar ilimi a yankin, wanda ke bukatar kulawar gaggawa.
Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya yi nuni da cewa, “Ilimi muhimmin abu ne a kowane fanni na rayuwar dan Adam, don haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wani malamin da ba ya zuwa makaranta”.
Ya yi nuni da cewa, akwai mutane da dama wadanda suka kammala karatu kuna ba su sami aiki ba, saboda haka za a iya daukarsu fomin maye gurbin wadanda ba sa son zuwa aiki.
Shugaban ya kuma shawarci matasan yankin da su sadaukar da kansu wajen samun ilimi mai inganci, domin cigaban rayuwarsu da kasa baki daya.
Ya kara da cewa, karamar hukumar karkashin jagorancinsa za ta ci gaba da bayar da tallafi ga ilimi, domin samar da ’ya’ya masu ilimi a nan gaba.
.
Usman Muhammad Zaria