NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu
Published: 30th, January 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ana ci gaba da zazzafar muhawara a shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya a kan batun samar da kotunan Shari’ar Musulunci.
Majalisar Ƙoli ta Harkokin Addinin Musulunci a yankin ce dai ta buƙaci hakan. Sai dai wasu ƙungiyoyi da ma ɗaiɗaikun mutane a yankin suna adawa da wannan buƙata.
Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokacin zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
ECOWAS Zata YI Taro A Ghana Don Tattauna Batun Niger, Mali Da Burkina Faso
Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fara taro a kasar Ghana don tattauna al-amura da suka shafi kasashen Niger Burkina Faso da kuma Mali.
Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa agendar taron nasu na kwanaki biyu, sun hada da huldar kungiyar da kasashen uku, musamman cibiyoyin ECOWAS da suke cikin kasashen, sannan da batun kudaden fito na kashi 0.5% wanda kungiyarsu ta (AES) ta dorawa kayakin da suke shigowa kasashensu da sunan gudanar da kungiyarsu. Labarin yace kungiyar ECOWAS bata karban kudaden fito da Visa daga kasashen kungiyar gaba daya tun kafin kasashen uku su fita amma a halin yanzu su suna karba. Kasashen uku sun bayyana ficewarsu daga ECOWAS ne daga farkon wannan shekarar.
Daga karshe kungiyar ta bayyana cewa zata fidda tsarin tattaunawa da kasashen uku daya bayan daya don warware matsalolin da ficewar daga kungiyar suka haddasa.