Kasar Iran Ta Mayar Da Martani Ga Shawarar Shugaban Amurka Kan Tilastawa Falasdinawa Gudun Hijira
Published: 30th, January 2025 GMT
Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland.
Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa daga tushensu.
Arqchi ya kuma mayar da martani ga tashar ta Sky News kan tambayar ‘yancin da ‘yan sahayoniyya suke da shi na rayuwa, inda ya ce: “Kowane dan Adam na da ‘yancin rayuwa, amma babu wanda ke da hakkin ya mamaye kasar wani, wannan kasa ta Falasdinawa ce, dole ne Falasdinawa su yanke shawara da kansu game da makomar kasarsu”.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Habasha Da Somaliya Sun Tattaunawa Hanyoyin Sake Mayar Da Alaka
Fira ministan hakar Habasha Abiy Ahmed ya sami kyakkyawar tarba daga shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mamhud a birnin Mogadishu na Habasa a ranar Alhamis da ya kai ziyara domin bunkasa alaka a tsakainin kasashen biyu.
Sabani a tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna ya kunno kai ne a shekarar da ta gabata, bayan da kasar ta Habasha ya kulla yarjejeniya da yankin Somaliland akan tashar jirgin ruwa.
Ita dai kasar ta Habasha ba ta da iyaka da ruwa, don haka take son amfani da mashigar ruwan kasar ta yankin Somaliland. Habashan dai tana son gina wani yanki na kasuwanci a gabar ruwan ta yankin Somaliland.
Yankin Somaliland na kasar Somaliya ne wanda Mogadishu take daukar cewa ba kasa ce mai cin gashin kanta.
Somaliya ta nuna fushinta akan waccan yarjejeniyar tare da zargin Habasha da yin kuste a cikin iyakokin kasarta.
A cikin watan Disamba ne dai Turkiya ta fara shiga tsakanin kasashen biyu domin warware sabanin da yake a tsakaninsu.
Tattaunawar ranar Alhamis din a tsakanin kasashen biyu ta mayar da hankali ne akan kasuwanci, da tsaro da kuma batun sake mayar da alakar da diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.