Wata uku uami’o’i ba su da wutar lantarki —SSANU
Published: 30th, January 2025 GMT
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba.
Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na Naira dubu 70 da sauran sauye-sauye da ke tattare da shi zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar nan ta 2025.
Shugaban Ƙungiyar SSANU ta Kasa, Kwamred ohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a yayin taron Majalisar Tuntuba ta Ƙasa (NAC) da ƙungiyar ta gudanar a Abuja.
Kwamred Ibrahim ya bayyana cewa har yanzu Gwamantin Tarayya da na wasu jihohi ba su fara biyan ma’aikatan jami’a sabon albashin ba, duk da kasancewarsu ƙwararru a fannoni daban-daban.
Game da zargin ’yan Majalisar Dokoki ta Ƙasa da neman xin hancin Naira miliyan takwas daga kowane shugaban jami’ar Gwamnatin Tarayya kafin su amince da kasafin kuɗin makarantarsa, ƙungiyar ta ce idan har hakan ta tabbata, to za su yaƙi lamarin kai da fata.
Ya ƙara da “idan ta tabbata, to wannan babban abin takaici ne, don a halin yanzu babu wata jami’ar gwamnati da ake da isassun kuɗaɗen biyan kuɗin lantarki.
“Daga cikinsu akwai waɗanda rabonsu da amfani da wutar an fi wata uku. Ta daga ina za su samu kudin da za su ba ’yan majalisar cin hanci Naira miliyan takwas-takwas.
“Idan har wakilan da jama’a suka zaɓa domin su tabbatar da cewa makarantun sun samun cikakkiyar kulawa babu tauyewa ne za su dawo suna neman cin hanci daga wurinsu, lallai za mu ɗauki mataki.
“Ina tabbatar maka cewa majalisa ba ta fi ƙarfinmu ba, za mu yaƙe su, domin a mazaɓunmu suke, za samu kayar da su,” in ji shugaban na ma’aikatan jami’a.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Wutar Lantarki
এছাড়াও পড়ুন:
Al-Houthi : Isra’ila Na fakewa Da Goyan Bayan Amurka Tana Karya Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza
Shugaban kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen Sayyed Abdul-Malik Al-Houthi, ya bayyana cewa Isra’ila na fakewa da goyan bayan Amurka tana keta yarjeejniyar tsagaita wuta a Gaza.
Al-Houthi ya bayyana cewar: Kin janyewar makiya daga yankin Rafah, ya zamanto karara karya yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Masar da makiya yahudawan sahyoniya. »
Ya kara da cewa: gazawar ‘yan mamaya na janyewa daga yankin Rafah na nuni da wata barazana mai hatsari ga al’ummar Falastinu da gwamnati da sojojin Masar. »
Jagoran kungiyar ta Ansarullah ya jaddada cewa: Makiya ba su cika bangare mai yawa na alkawurran da suka dauka ba, musamman a fagen ayyukan jin kai, sannan kuma suna yin watsi da sauran alkawurran da suka dauka, musamman na ficewa daga yankin Rafah. »
Al-Houthi ya kara da cewa: Haka nan makiya yahudawan sahyoniya ba su janye gaba daya daga kudancin kasar Labanon ba, wanda ya zama mamaya da kuma barazana ga al’ummar kasar Lebanon da kuma keta hurimin kasar. »
Zamu zura ido mu gani, kuma dole ne mu kasance cikin shiri,” in ji jagoran kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen.