Gabashin DRC : Félix Tshisekedi Ya Sanar Da Maida Da Martani”
Published: 30th, January 2025 GMT
Shugaba Felix Tsisekedi na Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo ya bukaci hadin kai na al’ummar kasar tare da sanar da mayar da martini kan rikicin gabashin kasar dake da nasaba da kungiyar ‘yan tawaye ta M23.
A yayin wani jawabi ga al’ummar kasar, shugaban na Kongo ya yi kira da a hada kai tare da ba da tabbacin cewa “ana ci gaba da mayar da martini kuma an karfafa tsarin tsaro.
” Ya kuma yi tir da gazawar kasashen duniya da kasancewar dubban sojojin Rwanda a kasar tare da bayyana kungiyar ta M23.
Wannan dai shi ne karon farko da shugaban na Kwango ke magana tun bayan harin da ‘yan tawayen suka kai a gabashin kasar a garin Goma.
Yayin jawabin shugaban na Kwango ya kuma ce suna goyon bayan hanyar tattaunawa.”
Félix Tshisekedi ya kuma yaba wa sojojin da suka fadi a fagen daga.”
Kungiyar M23 da ke samun goyon bayan sojojin Rwanda kimanin 3,000 zuwa 4,000, a cewar MDD, ta shafe fiye da shekaru uku tana fafatawa da sojojin Kongo a yankin, amma sun kutsa a cikin Goma babban birnin gabashin kasar a daren ranar Lahadi zuwa Litinin ga watan Janairun nan inda suka mamaye tsatsa dama.
Akalla mutane 100 ne suka mutu sannan wasu sama da 1,000 suka jikkata, a cewar rahotanni daga asibitoci da dama.
Halin da ake ciki na jin kai yana da matukar damuwa, in ji Majalisar Dinkin Duniya, inda ta sanar da cewa dole ne a dakatar da rarraba kayan agaji saboda yanayin tsaro.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Saboda Rikicin Kasar Sudan Ta Kudu Shugaba Musaveni Ya Isa Birnin Juba
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya isa birnin Juba na kasar Sudan ta kudu a yau Juma’a, a kokarin lalubo hanyar warware dambaruwar siyasar da kasar take ciki da hana barkewar sabon yakin basasa.
Jim kadan bayan yi wa mataimakin shugaban kasar Riek Machar daurin talala a gidansa ne kasar ta shiga zaman dar-dar da fargabar sake komawa cikin yakin basasa.
Da akwai kawance a tsakanin shugabannin kasashen Uganda Mosaveni da kuma Silva Kiir na kasar Sudan Ta Kudu. Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai kasar ta Uganda ta aike da sojoji masu yawa zuwa kasar ta Sudan ta Kudu, domin bayar da kariya ga gwamnatin Juba.
Gwamnatin Salva Kir tana zargin Machar da cewa yana rura wutar wani sabon yaki a cikin kasar. A ranar Laraba ta makon da ya shude ne dai aka yi wa mataimakin shugaban kasar daurin talala a gidansa saboda fadan da ake yi a yankin Upper Nile tsakanin sojojin gwamnati da kuma masu dauke da makamai na rundunar “White Army”.
Tawagar tarayyar Afirkan da ta isa birnin Juba wacce ta kunshi majalisar dattijan nahiyar Afirka, a kokarin shawo kan rikicin da kasar ta fada.
Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar.