Nukiliya : Babu Wani ‘Musayar Sako’ Tsakaninmu Da Amurka_ Araghchi
Published: 30th, January 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya ce Tehran ba ta samu wani sako daga sabuwar gwamnatin Amurka dangane da tattaunawar janye takunkumin ba.
Abbas Araghchi ya fada a ranar Laraba cewa duk wani matakin shiga irin wannan tattaunawa ya ta’alaka kan kwarin gwiwar da gwamnatin Donald Trump take da shi.
Ministan ya ce Iran ta riga ta shiga tattaunawa da bangarorin Turai da ke cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015, kuma tana jiran Washington ta fayyace manufofinta.
“Ba a aika ko karbo wani sako na musamman ba tsakanin kasashen biyu ba; saidai abubuwan da muke ji a kafafen yada labarai kawai.”
An yi ta rade-radin cewa gwamnatin Trump ta yi musayar sakonnin sirri da Iran.
“A baya mun cimma yarjejeniya; Iran ta aiwatar da ita, amma su ne suka kawo cikas,” in ji Araghchi, yana mai nuni da ficewar Amurka daga yarjejeniyar a shekarar 2018 a wa’adin mulkin farko na Trump.
Bayan ficewarta ne kuma gwamnatin Amurka ta kakabawa Iran sabbin takunkumai a wani mataki na matsin lamba ga Iran, lamarin da ya fusata Iran ta shiga tafiye-tafiyenta tare da soke aiki da wasu bangarori na yarjejeniyar ciki har da tace urenium din dinta son rai.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Trump : “Mun yi ganawa mai kyau da Iran”
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawa tsakanin kasarsa da Iran ke gudana, yana mai bayyana ta a matsayin mai matukar kyau.
Da yake magana da manema labarai a fadar White House jiya litinin, Trump ya ce tattaunawa da akayi da jami’an Iran sun yi matukar inganci.
A ranar 12 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zagayen farko na tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a shiga tsakanin kasar Oman a birnin Muscat.
Haka zalika a ranar Asabar 19 ga watan Afrilu bangarorin sun yi wa ta biyu a birnin Rome na kasar Italiya, a shiga tsakanin kasar Oman.
kasashen biyu sun bayyana kwarin gwiwar cewa za a ci gaba da tattaunawa, inda za a sake gudanar da mataki na gaba a kasar Oman a ranar Asabar mai zuwa.
Kafin nan kwararu daga kasashen na Amurka da Iran zasu hadu a kasar Oman a gobe Laraba inda zasu tattauna game da shirin nukiliyar na Iran na zaman lafiya.