Kungiyar NLC ta kira zanga-zanga kan ƙarin kuɗin waya
Published: 30th, January 2025 GMT
Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ta kira zanga-zangar adawa da ƙarin data da kiran waya a Najeriya.
NLC ta umarci rassanta na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya da su shirya domin fara zanga-zangar daga ranar Takara 4 ga watan Fabrairu mai kamawa.
Ta bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce ganin an janye karin kashi 50% da aka yi wa kuɗin kiran waya da na data, da kuma adawa da tsadar rayuwa wadda ta jefa ’yan Najeriya cikin tasku.
Shugaban ƙungiyar, Joe Ajaero, ya bayyana cewa zanga-zangar zai zama gargaɗi ga shugabanni kan dore wa al’umma abin da bai dace ba sa rashin adalci.
“Wannan gangami zai yaƙi ƙare-ƙaren ganin dama rashin adalci da aka yi na man fetur da wutar lantarki da hauhawan farashin kaya alhali an bar mutane da albashin N70,000 wanda bai taka kara ya karya ba,” in ji shi.
Ya ci gaba da cewa, duk rassan NLC da ƙungiyoyin fararen hula da dangoginsu a shirye suke su shiga wanan yakjn aiki.
Don haka ya buƙaci hukumar sadarwa ta ƙasa da majalisar dokoki ta kasa su tattauna da masu ruwa da tsaki domin samun maslaha kan ƙarin kuɗin da suka tsara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yajin aiki zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
DG VON Yayi Kira Ga Zaman Lafiya Da Hadin Kai Don Fadada Ci gaban Tattalin Arziki Da Ci Gaba.
Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata.
Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a Minna jihar Neja.
Malam Jibrin Baba Ndace ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ya zama wajibi saboda nasarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu ya kasance nasarar mu baki daya, don haka akwai bukatar mu kasance cikin nasara.
Daga nan sai ya mika gaisuwar ban girma ga daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya na bikin sallah karama tare da shawartar su da su dage wajen tallafa wa aikin Nijeriya domin samun sakamako mai ma’ana.
A cewarsa a madadin daukacin mahukunta da ma’aikatan gidan rediyon Muryar Najeriya, ina mika sakon gaisuwa da jinjina ga daukacin al’ummar musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya a daidai lokacin da muke gudanar da bukukuwan karamar Sallah mai albarka tare da shawartar su da su aiwatar da abin da suka koya a cikin azumin watan Ramadan.
Malam Jibrin Baba Ndace ya yi addu’ar Allah ya karawa ‘yan Najeriya farin ciki da walwala, da kuma sabon karfi domin su ci gaba da hada kai wajen samar da fahimtar juna, wajen bayar da gudunmawa mai kyau ga ci gaba da zaman lafiyar Nijeriya.
PR ALIYU LAWAL