Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-04-23@01:31:42 GMT

Hisbah Ta Kama Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Aure A Asirce

Published: 30th, January 2025 GMT

Hisbah Ta Kama Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Aure A Asirce

Hukumar Hisbah ta damke wasu matasa a jihar Kano bisa laifin yin aure a asirce ba tare da sanin iyayensu ko amincewar iyayensu ba.

A cewar Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ma’auratan sun yi aure ne a wani wurin shakatawa bayan wani ya  dauki nauyin biyan sadaki.

Abubakar ya yi Allah-wadai da wannan  auren, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai dace da addinin Musulunci ba, kuma ba a yarda da shi ba.

“Hukumar ta kama ma’auratan kuma za ta ci gaba da bincike tare da kame abokansu da kuma wadanda suka taimaka wajen auren sirri.”

Abubakar ya yabawa wadanda suka sanar da hukumar auren sirri, sannan ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ba a yarda da shi ba+ ga hukumomin da abin ya shafa.

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar Hisbah ta jihar Kano na ci gaba da tabbatar da bin doka da oda a jihar.

Daga Khadija Aliyu

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Lebanon Sun Kama Wasu Mutanen Da Suke Shirin Cilla Makamai Kan HKI

Majiyar labarai daga kasar Lebanon sun bada sanarwa kama wasu mutane wadanda suke shirin Cilla Makamai kan HKI.

Jaridar Arab News ta yanar gizo ta kuma kasar Saudiya ta bayyana cewa a makon da ya gabata ma an kama wasu mutane wadanda ake zargi da cilla makaman roka kan HKI daga kudancin kasar ta Lebanon.

Amma dangane da kwance damarar kungiyar Hizbullah kuma shugaban kasar Lebanon Jesept Aun ya ce wannan al-amarin ba abu ne mai sauki ba, sai dai a jira lokacinda ya dace na yin hakan. Aun ya kara da cewa duk wani kokari na kwance damarar kungiyar hizbullah kawo karshen zaman lafiya a kasar Lebanon ne.

Kafin haka dai shugaban kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kasim a jawabin da ya gabatar a ranar Jumma’a ya bayyana cewa ba wanda ya ida ya kwace, makaman kungiyar amma kungiyar zata iya tattainawa don kyautata tsaron kasar Lebanon tare da sauran jami’an tsaron kasar.

Wasu masana suna ganin da alamun wasu jami’an gwamnatin kasar Lebanon sun zama wakilan HKI da Amurka a kasar. Musamman ganin yadda HKI ta kai hare-hare har sau 2700 bayan tsagaita bude wuta da kungiyar Hizbulla, ba zakat aba jin wani yayi magana a kansa ba, amma suna maganar kwance damarar kungiyar ta Hizbullah.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hajjin 2025: Kashim Shettima Ya Jinjinawa Hukumar Alhazai Bisa Matakan Da Ta Dauka
  • Iyalen Surajo Malumfashi na Radio Nigeria Kaduna Yana Gayyatar Jama’a Zuwa Daurin Auren ‘Yar Sa
  • Shettima Ya Gayyaci Shugaban NAHCON Da Mambobin Hukumar Kan Shirye-shiryen Hajjin 2025
  • Hisbah ta kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi
  • Hisbah A Katsina Ta Musanta Zargin Cin Zarafin Wata Budurwa A Wani Faifan Bidiyo
  • Sojojin Lebanon Sun Kama Wasu Mutanen Da Suke Shirin Cilla Makamai Kan HKI
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Bada Tallafin Kudi Ga Manoman Alkama
  • NDLEA ta kama hodar iblis da aka ɓoye cikin littafai ana shirin kaiwa Saudiyya
  • Ruftawar gini ta kashe mutum 5 a Legas
  • Tashin Gobara A Kwale-Kwale Ya Lashe Rayukan Mutane 143 A Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango