Masu ɗibar fetur daga tankar da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara hari
Published: 30th, January 2025 GMT
Masu ɗibar man fetur daga wata tankar mai da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara da ke hana su farmaki.
Bayan faduwar tankar a cikin dare man cikinta ya fara tsiyaya, inda motar ta kama da wuta a kan babbar hanyar Ogbomosho zuwa Ilorin a ranar Laraba.
Faɗuwar motar ke da wuya wasu mazauna yankin Kasuwar Sabo, da ke Orile Igbon, suka fara tururuwar zuwa ɗibar man.
Jami’an kashe gobara da suka zo aikin ceto bayan aukuwar hatsarin sun nemi hana mutanen zuwa ɗuban, amma sai mutanen suka bijire suma far musu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɗibar man fetur tankar mai
এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72
Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a Jihar Binuwai ya ƙaru zuwa 72.
Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.
Da farko a ranar Lahadi Gwamna Hyacinth Alia a yayin da yake jawabin Ista a wani coci, ya sanar a yayin cewa an gano gawarwaki 59.
Daga bisani aka gano ƙarin gawarwaki a cikin jejin yankunan da aka kai hare-haren.
Kakakin gwmanan jihar, Isaac Uzaan, ya bayyana cewa an gano ƙarin gawarwaki 12 a Ƙaramar Hukumar Uku sauran mutum ɗaya kuma a Logo.
Tsakanin daren ranar Alhamis da safiyar Juma’a ne kai hare-hare a ƙauyukan yankin Sankera wanda ya ƙunshi ƙananan hukumar Ukum, Logo, and Kastina-Ala.