Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa
Published: 30th, January 2025 GMT
Kamfanin Meta, mamallakin Facebook, ya amince zai biya dala miliyan 25 don sasantawa kan shari’ar da Donald Trump, ha shigar game da rufe masa shafinsa.
Trump, ya maka Meta a kotu a shekarar 2021 bayan da Facebook ya rufe shafinsa sakamakon harin da aka kai Majalisar Dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairu.
Kaso mafi tsoka na kuɗin wanda ya kai dala miliyan 22—zai tafi ne wajen gina ɗakin karatu na Trump, yayin da sauran ƙudin za a biya lauya da wasu mutane da suka shigar da ƙarar tare da shi.
Trump, ya kuma maka Twitter (wanda yanzu ake kira X) da YouTube a kotu saboda rufe shafukansa, amma kotu t kori ƙarar.
A baya, Facebook ya dakatar da Trump saboda yaɗa labaran ƙarya kan zaɓen Amurka na 2020, amma daga baya ta rage takunkumin zuwa shekaru biyu, sannan ta dawo masa da shafukansa a shekarar 2023.
Rahotanni sun ce tattaunawar sulhu ta fara ne a watan Nuwamban 2024 lokacin da Shugaban Kamfanin Meta, Mark Zuckerberg, ya gana da Trump a gidansa na Mar-a-Lago.
Bayan wats tattaunawa da suka yi a watan Janairun 2025, Meta ta amince da cire wasu takunkumai da aka ƙaƙaba wa shafukan Trump.
Trump, wanda shi ne sabon shugaban Amurka, a baya ya yi amfani da shafukansa na sada zumunta wajen jadadda iƙirarin cewar shi ne ya lashe zaɓe 2020 da aka gudanar a ƙasar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Mark Zuckerberg
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji sun kama shugaban ’yan bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu a Zamfara
Dakarun Sojin ‘Operation FANSAN YANMA’, sun kama Ƙasurgumin Shugaban ’Yan Bindiga, Kachallah Hassan Nabamamu, wanda ya addabi al’ummar Mada, Tsafe, da wasu yankunan Jihar Zamfara.
Dakarun sun kai farmaki Hegin Mahe, Ruwan Bore, garin Mada, a Ƙaramar Hukumar Gusau a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Cibiyar bincike ta nemi a tabbatar da dokar kare haƙƙin mata a Arewa Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan KanoBayan musayar wuta, sojoji sun kashe wasu ’yan bindiga, yayin da Nabamamu ya tsere zuwa cikin wani gida, amma daga ƙarshe dakarun suka cafke shi.
Bayan kama shi, ɗaya daga cikin yaransa, Bakin Malam, ya jagoranci kai harin ramuwar gayya wasu ƙauyuka, wanda ya tilasta wa mazauna ƙauyukan tserewa.
Sai dai dakarun sun mayar da martani, inda suka fatattaki ’yan bindigar, tare da ƙara jibge sojoji don tabbatar da tsaro a yankin.
Nabamamu, ya kasance almajiri ne, daga baya ya zama hatsabibin ɗan bindiga wanda ya yi sanadin ajalin mutane masu yawan gaske.
Ya jagoranci sama da mayaƙa 100, inda yake karɓar haraji daga hannun mazauna wasu ƙauyuka, kuma yana da alaƙa da masu yi wa wasu mahara safarar makamai a yankin.
Kama shi na iya rage ƙarfin ’yan bindiga a Zamfara, yayin da sojoji ke ƙara ƙaimi domin kawar da barazanar tsaro da tabbatar da zaman lafiya a yankin.