Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok
Published: 30th, January 2025 GMT
Baloch ya ce “Na amince da laifin kashe ‘yata, saboda abinda take yi, zubar da mutuncin dangina ne.”
‘Yansandan dai tuni suka sanya shari’ar cikin wani lamari na ‘kisan mutuntaka’, wacce al’ada ce ga ‘yan uwa, musamman maza, ke kashe mata, wanda suke imanin cewa, sun kawo “abin kunya” ga danginsu.
.এছাড়াও পড়ুন:
Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72
Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai a Jihar Binuwai ya ƙaru zuwa 72.
Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.Adadin ya ƙaru ne bayan gano ƙarin gawarwaki 13 a ranar Litinin a ƙananan hukumomin Ukum da Logo.
Da farko a ranar Lahadi Gwamna Hyacinth Alia a yayin da yake jawabin Ista a wani coci, ya sanar a yayin cewa an gano gawarwaki 59.
Daga bisani aka gano ƙarin gawarwaki a cikin jejin yankunan da aka kai hare-haren.
Kakakin gwmanan jihar, Isaac Uzaan, ya bayyana cewa an gano ƙarin gawarwaki 12 a Ƙaramar Hukumar Uku sauran mutum ɗaya kuma a Logo.
Tsakanin daren ranar Alhamis da safiyar Juma’a ne kai hare-hare a ƙauyukan yankin Sankera wanda ya ƙunshi ƙananan hukumar Ukum, Logo, and Kastina-Ala.