Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
Published: 30th, January 2025 GMT
Isra’ila ta dakatar da sakin fursunonin Palasɗinawa ba zato ba tsammani yayin da ake ci gaba da musayar fursunoni da waɗanda aka kama ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a cewar rahoton Army Radio.
Hukumomi ba su bayyana dalilin dakatarwar ba, kuma babu tabbas kan lokacin da za a ci gaba da tsarin.
Yarjejeniyar tsagaita wutar an ƙulla ta ne don bayar da damar musayar fursunonin da Hamas ke riƙe da su da kuma waɗanda ke tsare a Isra’ila.
Sai dai wannan matakin ba zato ba tsammani ya haifar da rashin tabbas kan ci gaba da yarjejeniyar.
কীওয়ার্ড: Falasɗinawa Isra ila Musaya
এছাড়াও পড়ুন:
Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta yi watsi da rahoton da sojin Isra’ila suka fitar kan kisan da aka yi wa sama da jami’an agajin gaggawa na Gaza a watan da ya gabata, wanda gwamnatin kasar ta ce an kashe ne ta bisa kuskure.
Kungiyar ta yi fatali da rahoton na Isra’ila da cewa ba shi da inganci kuma ba za a amince da shi ba, tana mai jaddada cewa yana cike da karairayi.
A wani rahoto da suka fitar ka abinda ya faru sojojin Isra’ila sun yi ikirarin cewa, an samu ” kura-kurai da yawa” a kisan da akayi wa jami’an agajin a Gaza, suna masu cewa za a kori wani kwamandan sojoji.
“Binciken ya nuna cewa an samu wasu matsaloli na rashin da’a na kwararru, da rashin bin umarni, da kuma gaza yin cikakken bayani kan lamarin,” in ji rundunar.
A ranar 23 ga Maris, ne aka harbe wasu ma’aikatan agaji na Falasdinawa 15 da masu aikin ceto a kusa da Rafah da ke kudancin Gaza.
Sojojin Isra’ila sun sake nanata cewa shida daga cikin likitocin Falasdinawa 15 da Isra’ila ta kashe, ‘yan kungiyar Hamas ne.
Kisan da akayi wa jami’an agajin gaggawa na falasdinu ya fuskanci tofin Allah-tsine daga kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa da dama.
Lamarin dai ya sake fiddo a fili irin ta’asar da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza.
Da farko dai Isra’ila ta yi ikirarin cewa sun bude wuta ne, saboda yadda motocin suka nufo, a cikin dare, ba fitilu, kuma babu wata masaniya da sojinta suke da a kan zuwan motocin.
Amma kuma daga baya hukumar sojin ta ce, wannan bayani da ta bayar akwai kuskure, bayan da aka gano wani hoton bidiyo a wayar daya daga cikin ma’aikatan agajin da sojin Isra’ilar suka kashe a wannan hari, hoton da ke nuna motocin na tafiya da fitilu a kunne da kuma duk wata alama da za ta fayyace su waye.