Mahaifi ya harbe ’yarsa har lahira saboda wallafa bidiyo a Tiktok
Published: 30th, January 2025 GMT
Hukumomi a birnin Quetta na Ƙasar Pakistan, sun kama wani mutum mai shekaru 50, kan zargin kashe ’yarsa mai shekaru 15 a duniya, saboda ta ƙi daina ɗora bidiyonta a kafar TikTok.
Rahoton ’yan sanda ya nuna cewar, mutumin ya dawo da iyalinsa daga Amurka zuwa Pakistan kwanan nan kafin aikata kisan.
Hisbah ta kama masoya kan yin aure ba tare da amincewar iyayensu ba Wata uku uami’o’i ba su da wutar lantarki —SSANUYa amsa laifin harbe ’yarsa, inda ya ce tana aikata abubuwan da ba su dace da addini da al’ada ba, ta hanyar saka bidiyo a TikTok.
An kuma kama ɗan uwansa kan zargin taimaka masa wajen aikata laifin.
Dukkaninsu sun nuna rashin amincewa da yadda matashiyar ke amfani da TikTok, wanda suka ce hakan ya saɓa wa tarbiyya mai kyau.
A halin yanzu, kotu ta bayar da umarnin tsare su na tsawon kwanaki 10 don ci gaba da bincike.
Irin wannan kisa ya zama ruwan dare a Pakistan, inda ’yan uwa ke kashe mata kan wani abu da suke ganin ya saɓa wa al’ada ko zai jawo wa danginsu abun kunya.
Wannan lamari ya tashi hankalin jama’a kan yadda ake amfani da kafofin sada zumunta da kuma tasirin al’adu a tsakanin iyalai.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
MDD Ta CE Sake Tada Komatsar Tattalin Arzikin Kasar Siriya Zau Dauki Shekaru 50 Nan Gaba
MDD ta bada sanarwan cewa tattalin arzikin kasar Siriya na bukatar shekaru 50 nan gaba kafin ta koma kamar yadda take kafin yakin basasa a kasar.
Tashar talabijan ta Presstv ta nakalato shugaban hukumar UNDP Achim Steiner yana fadar haka a jiya Alhamis, ta kuma kara da cewa hukumar ta ta gudanar da bincike kuma ta gano cewa, rikici da yakin basasa da kuma mamayar kasar da sojojin kasashen yamma suka yiwa kasar, ya sa al-amura sun lalace a kasar, ta yadda idan tana bukatar komawa matsayinta kafin shekara ta 2011 tana bukatar rabin karni kafin hakan ya samu. Wato kasar Siriya ba zata koma kamar yadda take a shekara ta 2011 ba sai nan da shekara 2080.
Tace Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa a ko wace shekara kafin ta sami wannan ci gaban. A halin yanzu dai kasha 90% na mutanen kasar Siriya suna rayuwan talaka. Sannan kasha 50% daga cikinsu basa da aikin yi. Sannan tattalin arzikin kasar GDP na kasar yana rabin matsayinsa a shekara ta 2011. Banda tallafi daga kasashen waje kasar Siriya tana bukatar zuba jari mai yawa don komawa kamar yadda take.