Aminiya:
2025-03-03@09:38:00 GMT

Wani ya kashe ’yarsa saboda bidiyon TikTok a Pakistan

Published: 30th, January 2025 GMT

Wani uba a ƙasar Pakistan ya kashe ɗiyarsa matashiya bayan ta saka wasu faifan bidiyo da ya ɗauka a matsayin waɗanda ba su dace ba a manhajar sada zumunta ta TikTok, in ji ‘yan sanda a ranar Alhamis.

Shugaban ‘yan sandan yankin, Babar Baloch, ya ce mutumin wanda aka ce yana da shekara 50 a duniya, ya dawo da iyalansa daga ƙasar Amurka kwanan nan, domin su zauna a birnin Ƙuetta da ke Kudu maso Yammacin Pakistan.

Meta zai biya Trump $25m kan rufe shafinsa Jirage sun yi karo a sararin samaniya a Amurka

Mahaifin, wanda yanzu haka yake tsare, ya amsa laifin harbe ’yarsa a farkon wannan makon bayan ta ƙi sanya suturar da ta dace kuma ta daina sanya bidiyon da ‘yan uwanta suka ɗauka a matsayin “bidiyon marasa mutunci” akan TikTok, in ji Baloch.

‘Yan sanda na ɗaukar lamarin a matsayin kisan gilla.

Kimanin mata 1,000 ne ake kashe wa a Pakistan ta hannun danginsu, uba, ’yan’uwa da ’ya’yansu bisa zargin ceto mutuncin iyali, a cewar Hukumar Kare Haƙƙoƙin Ɗan Adam ta Pakistan (HRCP).

Kungiyar kare haƙƙin bil adama ta Amnesty International ta ce waɗanda suka kashe a mafi yawan lokuta suna tserewa hukunci saboda wata doka ta Musulunci a cikin dokokin da ke bai wa ’yan uwan ​​waɗanda aka kashe damar yafe wa wanda ya aikata laifin.

Pakistan ta amince da wata doka a shekara ta 2016 don kawar da wani ɓangare na magana mai cike da cece-kuce, amma hakan bai kai ga dakatar da wannan ɗabi’ar ba, a cewar HRCP.

 

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dakatar da Muƙaddashin Shugaban Ma’aikata kuma Babban Sakataren Tsare-Tsare, Salisu Mustapha, kan badaƙalar zaftare albashin ma’aikata ba bisa ƙa’ida ba.

An umarci Mustapha da ya sauka daga muƙaminsa na Babban Sakataren Tsare-Tsare a Ofishin Shugaban Ma’aikata domin ba da damar gudanar da bincike.

A gaban mijina Akpabio ya nemi kwanciya da ni —Sanata Natasha Buhari ya koma Kaduna da zama bayan shafe shekara 2 a Daura

Gwamna Abba ya amince da naɗa Malam Umar Muhammad Jalo, Muƙaddashin Babban Sakataren REPA, a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan jihar har zuwa lokacin da za a kammala binciken lamarin.

Matakin gwamna ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da dama da ma’aikatan gwamnati suka yi kan rage albashi ba bisa ƙa’ida da kuma jinkirin biyan albashi a kan lokaci.

A martaninsa, ya jaddada matsayin gwamnatinsa na rashin amincewa da duk wani rashin gaskiya da suka shafi harkokin kuɗi.

Ya kuma yi alƙawarin cewa duk wanda aka samu da hannu a lamarin za a hukunta shi.

“Wannan gwamnati ba za ta lamunci duk wani zalunci a kan ma’aikata ba. Duk wanda aka kama yana wawure albashin ma’aikata za a hukunta shi ba tare da la’akari da muƙaminsa ba,” in ji Gwamna Abba.

Domin shawo kan matsalar, gwamnan ya kafa kwamitin mutum bakwai wanda Kwamishinan Raya Karkara, Abdulkadir Abdussalam, zak jagoranta.

Gwamnan ya bai wa kwamitin umarni da ya duba albashin ma’aikata daga watan Oktoban 2024 zuwa Fabrairun 2025 domin gano waɗanda abin ya shafa, tantance asarar kudade, da bayar da shawarwari kan matakin da ya dace a ɗauka.

An umarci kwamitin da kammala bincikensa cikin kwanaki bakwai tare da gabatar da cikakken rahoto.

An naɗa Salisu Mustapha a matsayin Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan jihar a farkon wannan wata bayan Shugaban Ma’aikata jihar, Abdullahi Musa, ya tafi hutun jinya zuwa ƙasar Indiya domin neman magani.

Gwamna Abba ya tabbatar wa ma’aikatan Jihar Kano cewa gwamnatinsa na da niyyar kasancewa adala, mai gaskiya, da kuma biyan albashi a kan lokaci.

Ya gargaɗi duk wani jami’in gwamnati da ke da hannu a badaƙalar kuɗi cewa zai fuskanci fushin doka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Miji ya kashe matarsa saboda abincin buɗa-baki a Bauchi
  • Nijar: An Kashe Sojoji 11 A Wani Hari Na Kungiyar al-Ka’ida
  • Zelensky : Ban Ga Laifin Da Na Yi Wa Trump, Ballantana In Nemi Afuwa
  • Masana’antar Kannywood: Da Tsohuwar Zuma… -Fassarar Farfesa Uba Adamu
  • Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da tsira daga wuta
  • Falalar Ramadan: Wata na rahama, gafara, da ‘yanci daga wuta
  • Wata Mujalla Ta Zabi Shugaban NPA A Matsayin Gwarzonta Na Shekarar 2025
  • Rage Albashi: Abba ya dakatar da muƙaddashin shugaban ma’aikatan Kano
  • An kori ma’aikatan Microsoft saboda adawa da yahudawan sahyoniya
  • Shugaban kasar Guinea-Bissau a ya yi wata ganawa da shugaban kasar Rasha