An Harbe Mutumin da Ya Ƙona Al-Ƙur’ani A Sweden
Published: 30th, January 2025 GMT
Mista Momika ya yi zanga-zanga da dama da ke nuna ƙin jinin Musulunci, lamarin da ya haddasa bore a ƙasashe da dama.
A lokacin da ya ƙona Al-ƙur’ani, an yi bore a ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza, inda aka kori jakadan ƙasar daga birnin.
Gwamnatin Sweden ta ce ta ba shi izinin yin zanga-zangar, bisa hujjar cewa yana da ‘yancin faɗar albarkacin baki, kamar yadda dokar ƙasar ta tanada.
কীওয়ার্ড: Salwan Momika
এছাড়াও পড়ুন:
SAHUR [Falalarsa Da Fa’idojinsa] Na 1
1.1 Abinci sahur yana da albarka; yin sahur albarka ne, haka ma abincin sahur abinci ne mai albarka.
Ana karɓo hadisi daga Miƙdãm ɗan Ma’adikarib Allah ya ƙara yarda a gare shi, daga Annabi (S.A.W) ya ce: “Ina horonku da cin abincin sahur, domin abinci ne mai albarka” Nasã’i (Almujtabã 4/149 da Sunanul Kubrã 2/115) da Ahmad (Musnad #17192) da salsala ingantacciya.
An karɓo daga Abud Dardã’i Allah ya ƙara yarda a gare shi, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Shi sahur abinci ne mai albarka.”Ibnu Hibban (Al’ihsãn #3464) Ɗabarãni (Mu’ujamul Kabir 17/131 hadisi mai lamba 322).
An karɓo daga Irbãdu ɗan Sãriyatu Allah ya ƙara yarda a gare shi ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya gayyace ni cin abincin sahur a cikin Ramalana sai ya ce: ” Tawo ka ci abinci mai albarka” Abu Dãwud (#2344) da Nasã’i (Almujtabã 4/148) da Ibnu Hibbãn (Al’ihsãn #3465) salsalar hadisin ingantacciya ce. A lafazin Nasã’i ya zo da ce: Na ji Manzon Allah (S.A.W) Yana gayyatar mutane cin abincin sahur a cikin Ramalana…
1.3 Allah yana yabon masu yin sahur, Mala’iku kuma suna yi musu addu’a.
An barɓo hadisi daga Abdullahi ɗan Umar, Allah ya ƙara yarda a gare su, ya ce: Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Lalle Allah yana yabon Mala’iku kuma suna addu’a ga waɗanda suke yin sahur” Ibnu Hibbãn (Al’ihsãn #3467) da Ɗabarani (Mu’ujamul Ausaɗ 6/287) da salsala ingantacciya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp