Leadership News Hausa:
2025-04-22@18:23:40 GMT

Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10

Published: 30th, January 2025 GMT

Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10

Sowore, wanda ya taɓa tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa, na fuskantar tuhume-tuhume guda 17 daga rundunar ‘yansanda, ciki har da laifi a kafafen sada zumunta da kuma kiran Shugaban ‘Yansanda na ƙasa, IGP Kayode Egbetokun, da “IGP na ƙarya.”

.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Zaɓen 2027: An soma liƙa fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamnan Bauchi

A ranar Litinin ɗin nan aka wayi gari da fastocin takarar shugaban ƙasa a Zaɓen 2027 na Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed.

An liƙa fastocin wuri-wuri da suka haɗa da shataletale da turakun wutar lantarki da allunan tallace-tallace daban-daban a wasu manyan tituna da ke ƙwaryar birnin na Bauchi.

HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato Bikin Ista: Hatsarin mota ya laƙume rayuka 5 a Gombe

Aminiya ta ruwaito cewa fastocin masu ɗauke da saƙon “Kaura for President” an manna su a wasu manyan hanyoyi da suka haɗa da titin jirgin ƙasa, Sabon Titin Karofi da kuma Ƙofar Dumi.

Ɗaya daga cikin matasan da ke aikin manna fastocin, Aminu Auwal, ya shaida wa Aminiya cewa wasu ’yan siyasa biyu — Ya’u Ortega da Talolo — ne suka ba su kwangilar.

Auwal ya ce: “an ba mu kwangilar liƙa fastocin gwamnan a manyan hanyoyi da ke cikin birnin Bauchi.

“Tun wurin ƙarfe 1:00 na dare muka fara wannan aiki kuma muna sa ran kammalawa a yau [Litinin].”

Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin ’yan siyasar biyu da suka ba da wannan kwangilar ya ci tura har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • 2027: Fastocin Takarar Shugaban Ƙasa Na Gwamnan Bauchi Sun Bayyana
  • NAJERIYA A YAU: Mene ne Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Kundin Tsarin Mulkin Najeriya?
  • Tinubu Ya Komo Nijeriya Bayan Ziyarar Mako 3 A Turai
  • Zaɓen 2027: An soma liƙa fastocin takarar shugaban ƙasa na Gwamnan Bauchi
  • Hukumar Kula Da Kasuwa: Adadin Kamfanoni Masu Zaman Kansu A Kasar Sin Ya Zarce Miliyan 57