Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya mika gaisuwar sabuwar shekara da fatan alheri ga kasar Sin yayin da ta shiga sabuwar shekarar gargajiya. Cikin sakonsa a jiya Laraba, Cyril Ramaphosa ya bayyana kwarin gwiwar shekarar Maciji za ta ci gaba da karfafa matsayin Sin na karfin samar da kyawawan abubuwa da hikima da wadata na bai daya ga duniya.

Shi ma a jiyan, shugaban Zambia Hakainde Hichilema, ya aikewa shugaban kasar Sin Xi Jinping gaisuwar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar, yana mai fatan samun ci gaban kasashen da al’ummominsu.

Kotu Ta Bayar Da Belin Sowore Kan Naira Miliyan 10 Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje

A ranar Talata kuma, shugaban Angola Joao Lourenco ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga gwamnati da al’ummar Sinawa, yana mai fatan karfafa dangatakar kasarsa da Sin.

Shi ma shugaban Maldives Mohamed Muizzu, ba a bar shi a baya ba, domin a jiya Laraba ya aikewa takwaransa Xi Jinping da al’ummar Sinawa gaisuwa da fatan alheri a sabuwar shekara. Ya kuma yi fatan sabuwar shekarar za ta kawowa al’ummar Sin wadata da koshin lafiya da farin ciki. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Na Hasashen Samun Karin Yabanya A Shekarar 2025

 

Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da adadin yabanya ke karuwa a cikin gida, kuma karuwar bukatunsu ke raguwa, akwai hasashen raguwar bukatar shigo da nau’o’in amfanin gona cikin kasar daga ketare. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kungiyar BRICK Ta Rattaba Hannu A Kan Yarjeniyar Raya Ayyukan Noma A Duniya
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Shugaban Kasar Iran Ya Aike Da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Papa Roma Farancis
  • Sin Na Hasashen Samun Karin Yabanya A Shekarar 2025
  • Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Zababbun Shugabannin Gabon Da Ecuador
  • Inganta Kiwon Lafiya: Gwamna Buni Ya Ziyarci Sabuwar Cibiyar Sayar Da Magunguna Da Ke Damaturu
  • Idan Shugaban Kasar Siriya Mai Ci Ya Taka Kasar Iraki Ana Iya Kama Shi
  • Demokradiyyar Kwango Ta Haramta Jam’iyyar Josept Kabila A Kasar Saboda Hulda Da Yan Tawaye
  • Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin
  • KOFIN DUNIYA: Za A Kara Yawan Kasashen Da Suke Bugawa Zuwa 64 A Shekarar 2030