Kamfanin dillancin labaran BBC ya bayyana cewa mutane 64 ne suke cikin jirgin fasinja na kamfanin American Airline, sannan mutane 3 ne a cikin jirgin yaki mai saukar ungulu samfurin Black Hawk suka yi karo a birnin washinton a safiyar yau Alhamis.

Labarin ya kara da cewa, a halin yanzu sun tashi daga kubutar da wadanda suke da rai zuwa neman gawaki kawai, tunda ana ganin da wuya a sami wani da rai a cikin fasinjojin jirgin.

Ya zuwa yanzu dai an tsamo gawakin mutane 30, kuma suna ci gaba da aikin gano wasu karin gawakin.

Jami’an gwamnatin kasar Amurka sun bayyana cewa jirgin fasinjar ya rabu zuwa kasha ukku sannan ya fada cikin wani ruwa mai zurfin mita 7.

Shugaba Trump dai ya bayyana cewa, hatsarin wanda za’a iya kauce wa ne, idan da kowa yayi aikin da ya dace. Don haka kuskuren dan’adama ne.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Kasar Masar Ta Tabbatrawa Falasdinawa, Tana Bayansu Kafin Taron Kasashe Larabawa

Gwamnatin kasar masar ta tabbatarwa gwamnatin Falasdinawa kan cewa tana goyon bayan falasdinawa a cikin dawo da hakkinsu, na kafa kasarsu mai cikekken yanci wacce take da gabacin birnin Qudus a matsayin babban birnin Kasar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mostafa Madbouly ministan harkokin wajen kasar Masar yana fadar haka a lokacin ganawarsa da tokwaransa na gwamnatin Falasdinawa a Ramallah Mohammada Mustafa a birnin Alkahira.

Madbouly ya kara da cewa gwamnatin kasar Masar tana son ganin an gaggauta sake ginza Gaza da kuma maida rayuwa kamar yadda take a gaza da gaggawa.

Ya ce kasashen larabawa ba zasu taba yarda da kasar Falasdina kasa da yarjeniyar 4 ga watan Yunin shekara ta 1967.

A ranar Talata 4 ga watan Maris da muke ciki ne za’a gudanar da taron gaggawa na kungiyar kasashen larabawa a birnin Alkahira na kasar Masar don tattauna halin da Falasdinawa suke ciki musamman a Gaza da kuma yankin yamma da kogin Jordan.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ramadan: Hon Jaji Ya Ƙaddamar Da Tallafin Abinci Ga Mutane Sama Da 500,000 A Zamfara
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • Nijar: An Kashe Sojoji 11 A Wani Hari Na Kungiyar al-Ka’ida
  • Hamas Ta Bukaci Falasdinawa A Birnin Qudus Su Sabawa Dokar Takaita Yawan Masu Shiga Masallacin Al-Aksa A Kudus
  • Kasar Masar Ta Tabbatrawa Falasdinawa, Tana Bayansu Kafin Taron Kasashe Larabawa
  • Kasashen Afirka ta Kudu da Malaysia da Colombiya za su hana jiragen ruwa da ke dauke da makamai zuwa Isra’ila
  • Xi Ya Jaddada Ciyar Da Shirin Kasar Sin Mai Kwanciyar Hankali Zuwa Babban Mataki
  • Yadda farashin kayan abinci ya sauka a kasuwannin Arewa
  • Girke-girkenmu Na Azumi
  • MDD Ta Bayyana Cewa Yara Fiye Da 100,000 Ne Suka Ka Yi Rijistan Fara Karatu A Makarantun Gaza Na Sabuwar Shekarar Karatu