Aminiya:
2025-03-03@21:26:29 GMT

Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe

Published: 30th, January 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, sun kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar dabbobi.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Abdulkadir Tukur mai shekara 35 da Ibrahim Saidu mai shekara 20.

KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai

An same su da tumaki 28 da awaki 57, jimillar dabbobi 85 da ake zargin da sato su.

An kama su ne a ranar 25 ga watan Janairu, 2025, bayan da Dagacin Tulmi a Ƙaramar Hukumar Akko, Abubakar Umar, ya kai wa ‘yan sanda rahoto.

Wani mafarauci mai suna Yayaji Muhammad ne ya tare su a garin Tulmi, inda suka kasa bayar da cikakken bayani kan dabbobin da ke tare da su.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi, ya ce jami’an ofishin Pindiga sun karɓi rahoton tare da fara bincike.

Ya ce waɗanda ake zargi sun amsa laifinsu, kuma har yanzu an mayar masu dabbobin guda 25 daga cikinsu.

Daga cikin mutanen da aka mayar wa dabbobinsu akwai Joseph Ahmadu da aka mayar wa da awaki shida, Bello Sintali da ya samu awaki huɗu, Godwin Iro da aka mayar wa da awaki 10, da Zaraya Jepter da aka dawowa da awaki biyar.

Dukkaninsu sun fito ne daga Jurara yankin Kashere da wasu ƙauyuka a ƙananan hukumomin Akko da Billiri.

Haka kuma, wasu mutum huɗu da ake zargi da hannu a satar dabbobin sun tsere.

Waɗanda suka tsere sun haɗa da Rabe Saidu, Hamisu Saidu, Bode Saidu, da Wada Saidu, dukkaninsu daga ƙauyen Dawo a Ƙaramar Hukumar Kwami.

’Yan sanda na ci gaba da ƙoƙarin kamo su tare da ƙwato sauran dabbobin da aka sace.

DSP Buhari Abdullahi, ya tabbatar wa jama’a cewa suna ci gaba da bincike, kuma dabbobin da aka sace suna hannun ’yan sanda a matsayin shaida.

Ya ce dukkanin waɗanda ake zargin za a gurfanar da su a kotu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, ya buƙaci jama’a su kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suke zargi domin taimakawa wajen tabbatar da doka da oda a jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda zargi da ake zargi

এছাড়াও পড়ুন:

Wasu Kasashen Musulmi Sun Fara Azumin Ramadana A Yau Asabar, Yayin Da Wasu Za Su Fara A Gobe Lahadi

Daga cikin Kasashen  da su ka fara azumi a yau Asabar, da akwai Saudiyya, Katar, Hadaddiyar Daular Larabawa, Omman, Bahrain da Kuwait. Saikuma Masar, Syria, Falasdinu, Yemen, Sudan,Somaliya, Libya, Tunisa da kuma Aljeriya.

Kasar Moroko kuwa ta sanar da cewa, yau Asabar ne cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon Ramadan.

A kasar Iraki, ofishin dake kula da wuraren addini na Ahlussunnah, ya sanar da cewa, yau ne farkon Ramadan, yayin da ofishin babban marji’in shi’a Sayyid Ali Sistani ya sanar da cewa gobe Lahadi ne farkon Ramadan.

A nan  Iran ma dai an sanar da rashin ganin wata a fadin sassan kasar a daren jiya Juma’a, don haka yau Asabar zai zama cikon watan Sha’aban, gobe Lahadi zai zama farkon watan Ramadana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Rufe Makarantu  A Ramadan Ya Tauye Ƴancin Ɗalibai – CAN
  • Hisba ta kama wasu matasa ba sa azumi a Kano
  • Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa
  • Kasashen Somaliya Da Habasha Suna Gab Da Rattaba Hannu Akan Amfani Da Tashar Jirgin Ruwa
  • An kama ɓarayin waya a Kano
  • Gobara ta ƙone sashen wani asibiti a Legas
  • Tsohon shugaban hukumar NYSC ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
  • Wasu Kasashen Musulmi Sun Fara Azumin Ramadana A Yau Asabar, Yayin Da Wasu Za Su Fara A Gobe Lahadi
  • Ramadan: Saudiyya ta bai wa Kano da wasu jihohi kyautar dabino katan 1,250
  • Habasha Da Somaliya Sun Tattaunawa Hanyoyin Sake Mayar Da Alaka