Manoman Shinkafa Za Su Amfana Da Shiri Na Musamman Da Gwamnatin Jigawa Ta Bullo Da Shi
Published: 30th, January 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Jigawa ta bukaci manoman shinkafa da su hanzarta gyaran gonakinsu domin samun damar shiga shirin noman shinkafa da Gwamna Umar Namadi ya bullo da shi domin samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.
Mai bai wa Gwamna shawara kan shirin Noma Dan Riba, Alhaji Muhammad Idris Danzomo ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Dutse.
Ya ce bukatar ta zama wajibi domin bai wa manoman damar amfana da tsare tsaren gwamnati na bunkasa noman shinkafa da samar da ayyukan yi ga al’umma.
Alhaji Muhammad Idris Danzomo ya kuma shawarci manoman na shinkafa da su tabbatar sun tona rijiya a gonakinsu.
A cewar sa, za a tura malaman gona zuwa lungu da sako domin zakulo manoman shinkafar da suka shirya domin cin gajiyar sharin.
Bunkasa aikin gona dai na daya daga cikin kudirori 12 na Gwamna Umar Namadi na bunkasa tattalin arzikin al’umma da na gwamnati.
Usman Mohammed Zarian
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Jigawa
এছাড়াও পড়ুন:
Xi Ya Jaddada Ciyar Da Shirin Kasar Sin Mai Kwanciyar Hankali Zuwa Babban Mataki
Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya jaddada kokarin sa kaimi ga ciyar da shirin kasar Sin mai kwanciyar zuwa matsayi mai girma.
Xi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron nazari na ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS a jiya Juma’a. Inda ya yi kira da a ci gaba da kokarin kyautata zaman lafiya a kasar, al’umma su kasance cikin tsari, da kara inganta gudanar da mulkin kasar, kuma jama’a su samu karin gamsuwa. (Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp