Aminiya:
2025-04-26@09:44:56 GMT

Gwamnan Filato ya kori kwamishinoni 5

Published: 30th, January 2025 GMT

Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya kori kwamishinoni guda biyar daga muƙamansu.

Wannan ma cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Architect Samuel Jatau, ya fitar da yammacin ranar Alhamis.

Ɓarayin dabobbi sun shiga hannu, an ƙwato awaki 85 a Gombe Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai

Sanarwar ta bayyana cewa sauke kwamishinonin na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka, sai dai ba a bayyana dalilin korarsu ba.

Sanarwar ta bayyana cewa korar kwamishinonin ba zai rasa nasaba da gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba, musamman ganin yadda suka kwashe shekara guda wajen gudanar da ayyukansu.

A cewar wata majiya, gaza yin aiki yadda ya kamata ne ya sa aka cire su daga muƙamansu.

Kwamishinonin da aka sauke sun haɗa da: Chrysanthus Dawam, wanda ke riƙe da ma’aikatar kasafin ku6di da tsara tattalin arziƙi, Noel Nkup, wanda ke jagorantar ma’aikatar matasa da wasanni.

Ragowar sun haɗa da Jamila Tukur, Kwamishinar ma’aikatar yawon buɗe ido, Obed Goselle, wanda ke kula da ma’aikatar kimiyya da ƙere-ƙere, da Sule Musa, wanda ke jagorantar ma’aikatar ciniki da masana’antu.

Wannan mataki ya ɗauki hankalin al’umma, musamman mazauna jihar, inda ake ta hasashe kan yadda sauke kwamishinoni guda biyar zai shafi gudanar da ayyukan gwamnatin jihar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gwamna Calen Kwamishinoni

এছাড়াও পড়ুন:

2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba

Kujeru dubu daya da dari hudu da bakwai ne aka ware wa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Taraba domin maniyyata bana.

 

Babban Sakataren Hukumar mai barin gado Umar Ahmed Chiroma ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matakin da ake na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 ba tare da tangarda ba.

 

Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma Musulmin muminai na gudanar da aikin Hajji a kowace shekara akalla sau daya a rayuwarsu.

 

Chiroma ya ce hukumar ta kai wani mataki na ci gaba ta fannin shirye-shirye kamar yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ya ce sama da maniyyatan jihar 500 ne suka kammala biyan kudadensu.

 

Alhaji Ahmed Umar Chiroma ya kara da cewa a halin yanzu sama da Alhazai dubu biyar ne suka biya kudin aikin Hajji, yana mai kira ga sauran maniyyatan da su gaggauta biya domin cika wa’adin da hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta kebe.

 

Ya yi bayanin cewa hukumar ta samu karancin masu zuwa aikin hajjin ba, inda ya danganta hakan ga tabarbarewar tattalin arziki ganin yadda amfanin gona da shanu suka ragu matuka a farashi.

 

Sakataren zartarwa ya bayyana manoma da makiyaya a matsayin manyan masu biyan kujerun aikin Hajji a jihar, inda ya nuna cewa gwamnatin jihar ta biya kujeru hamsin (50).

 

Chiroma ya ci gaba da bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara yin alluran rigakafi da tantance maniyyatan da ke shirin kammala shirye-shiryen aikin Hajji.

 

A cewarsa, hukumar ta kammala shirye-shirye a sansanin Alhazai a Jalingo, babban birnin jihar.

 

Sakataren zartarwa mai barin gado ya bayyana karara cewa jami’an hukumar sun ziyarci kasar Saudiyya inda suka samu masaukin da suka dace da mahajjatan jihar Taraba.

 

Umar Ahmed Chiroma ya yabawa Gwamna Agbu Kefas bisa daukar nauyin Alhazai hamsin, yana mai jaddada cewa wannan karimcin zai taimaka matuka wajen taimakawa mutane da dama wajen gudanar da aikin hajjin 2025.

 

 

Sani Sulaiman

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Cazar Kudade Da Yawa Ke Haifar Da Raguwar Fitar Da Kaya A Tashoshin Jiragen Ruwa – NPA
  • Gwamnatin Katsina Ta Sauya Masu Yi Wa Alhazai Hidima A Saudiyya
  • Gwamnan Kano ya kafa sabbin hukumomi 4
  • Yobe na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya mafi zaman lafiya – Buni
  • Gwamnatin Haramtacciyar Isra’ila Tana Azabtar Da Falasdinawa A Gidajen Kurkukunta
  • An Umurci Sojoji Su Kawarda ‘Yan Bindiga Daga Kwara Da Niger A Cikin Wata Daya
  • 2025: NAHCON Ta Ware Kujerun Aikin Hajji 1,407 Ga Jihar Taraba
  • An Bayyana Filin Jirgin Sama Minna a Matsayin Mafita Ga Jiragen da ke sauka Abuja
  • Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
  • Aljeriya ta yi gagarimar korar bakin haure a rana guda zuwa Nijar