Shugaba Tinubu Ya Jinjinawa ‘Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje Bisa Nuna Halin Dattaku
Published: 31st, January 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa rahotanin da ya samu game kyawawan dabi’u da ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje suke nunawa a kasashen da suke, yana mai cewa hakan zai zaburar da matasa kan dabi’un da ke kara martabar kasa.
Shugaban ya yabawa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje yayin da ya karbi wasiku daga jakadan kasar Kanada a Najeriya, Pasquale Salvaggio, da jakadan Saliyo, Dr Julius F.
Har ila yau, shugaba Tinubu ya karbi wasikun amincewa da nuna gamsuwa daga Legesse Geremew Haile, jakadan kasar Habasha a Najeriya, da Archbishop Michael Francis Crotty, shugaban Bishop Bishop na fadar Vatican a Najeriya.
Babban Kwamishinan na Kanada ya shaida wa Shugaba Tinubu cewa ’yan Najeriya suna da himma a fannin ilimi, da wasannin motsa jiki, da kimiyya, da lafiya, da kasuwanci a kasarsa.
Ya ce ‘yan Najeriya a Kanada suna nuna kyawawan dabi’u da wayewa, da kwazo yayin cimma burinsu.
Salvaggio, wanda a baya ya yi aiki a Ghana da Cote’Ivoire, ya ce Kanada na neman fadada sha’awarta a kan man fetur da iskar gas, da al’amuran da suka shafi fasahar zamani, da noma, a dangantakar ta Najeriya.
Shugaba Tinubu ya yaba da nasarorin da ‘yan Najeriya suka samu a kasashen waje, yana mai bayyana su a matsayin abin zaburarwa ga mutane da dama.
A wani taron da ya yi da babban jakadan Saliyo kuwa, shugaba Tinubu ya tabbatar da cewa, muradin Najeriya na ci gaban gabar tekun Yamma da Afirka shi ne abin da ya sa a gaba.
Shugaban ya shaida wa jakadan cewa jarin da Najeriya ta yi a Saliyo na tsawon shekaru da dama ya taimaka wajen ci gaban Afirka da kuma inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Jakadan ya godewa shugaban kasar bisa goyon bayan da Najeriya ke bayarwa wajen cigaban kasarsa.
Ya ce “A Saliyo, ‘yan Najeriya sun fi ‘yan kasar yin kasuwanci, yawancin malamai a makarantu ‘yan Najeriya ne, babu bambanci tsakanin dan Najeriya da dan Saliyo idan kana tafiya a kan titin Freetown.”
“Muna bukatar ci gaba da neman zaman lafiya a nahiyarmu, ya kamata mu hada karfi da karfe wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, kalubalen da muke fuskanta a Afirka shi ne rashin tsaro, wanda ke hana ci gaba, ba mu da wanda zai kawo mana zaman lafiya, ssai in mun yi aiki tukuru.” in ji shi.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: xYan Najeriya Mazauna kasashen waje Shugaba Tinubu ya yan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kuɗin da ake kashewa.
An saba a watan Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buɗa-baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki.
NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta Lafiyar Jiki DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son HaihuwaShirin Najeriya a Yau ya duba hanyoyin da za ku yi girke-girken da yawa yadda aka saba cikin sauki ba tare da kashe maƙudan kuɗaɗe ba.
Domin sauke shirin, latsa nan